Bilal Abdullah likita dan Iraƙi ya gurfana gaban kotu a London | Labarai | DW | 07.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bilal Abdullah likita dan Iraƙi ya gurfana gaban kotu a London

Dan kasar Iraqin nan da aka tuhume shi da hannu a yunkurin kai hare haren bam da bai yi nasara ba a biranen London da Glasgow, a yau asabar ya gurfana gaban wata kotu a London. An tuhumi Bilal Abdullah wanda likita ne dan shekaru 27 da haihuwa kuma haifaffen Birtaniya amma tashin Iraqi, da hannu da kulla wata makarkashiyar tayar da bama-bamai bayan da shi da wani mutum suka tuka wata jeep da suka cika ta da gas mai cin wuta, suka afkawa ginin shiga filin jirgin sama na Glasgow dake yankin Scotland. A zaman kotun dai a yau Abdullah ya tabbatar da sunansa ne da kuma ranar haihuwar sa. A ranar 27 ga wannan wata na yuli zai sake gurfana gaban kotu.