Bila´in Nargis ya cika shekara ɗaya | Siyasa | DW | 02.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bila´in Nargis ya cika shekara ɗaya

A kwana a tashi an cika shekara guda da abkuwar bila´in ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwar Nargis a ƙasar Bama

default

Bila´in Nargis


A kwana a ta tashi, yau shekara guda kenan daidai da abkuwar bila´in ambaliyar ruwan sama da kaɗawar guguwa mai ƙarfi da aka raɗawa suna Nargis a ƙasar Bama.

Ranekun biyu da ukku ga watan Mayu ne na shekara ta 2008, wasu mummunan tawagen bila´o´i na ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa, suka rutsa da yankin Irrawady na ƙasar Bama.

A ƙalla mutane 140.000 suka rasa rayuka, sannan kussan miliyan biyu da rabi suka rasa matsugunai sanadiyar wannan masifa.

Shekara ɗaya baya har yanzu tunanin wanda abun al´ajabi nacigabada mamamaye zukatan jama´ar yankin mussamman ƙananan yara inji Bernd Schell, jami´in ƙungiyar bada agaji ta Red Cross dake aiki a Bama:

"Akwai ƙananan yara marayu, wanda suka rasa ma´aifansu a cinkin bila´in Nargis.A yanzu da zaran sun ga an fara ruwa, sai su kiɓice su kasa fita waje , sannan su daina zuwa makaranta.Har yanzu akwai firgita da tsoro a cikin zukatansu."

Ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa sun taimaka wajen kwanta da hankulan mutanen da al´amarin ya rutsa da su.Ta fannin ƙananan yara,Majalisar Ɗinkin Duniya Duniya ta tanadi maluman makaranta na mussamman 2.400 domin wanke masu ƙwaƙƙwalwa ta yadda zasu manta da abunda ya faru.

A ɓangaren gine gine an gida matsugunnai masu yawa ga mutanen da suka yi asara gidaje, to saidai da dama har yanzu, na rayuwa cikin bukkoki, wanda ba da wata wata ba ruwa kan iya awan gaba da su.

Andrew Kirkwood na asusun bada agaji ga ƙananan yara wato Save the Children Fund, ya bayyana sakaci da Ƙungiyoyin tallafi na duniya suka nuna a kaasr bama:

"Bayan abkuwar bila´in Nargis, idan aka auna da sauran ƙasashen duniya ,Bama ke sahun baya ta fannin taimakon raya ƙasa.Da dama daga mutane da haɗarin ya rutsa da su sun koma matsugunansu, ba tare da samun tallafi ba, suna fama da ƙuncin rayuwa.

Akwai buƙatar a dubi matsalarsu da idon rahama."

Ƙiddidigar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya, ta gano cewar kashi 11 cikin ɗari kawai na jama´a yankin Irrawady ,suka sami tallafi irin yadda ta kamata, bayan abkuwar bila´in Nargis.

Ƙungiyar bada agaji ta "Medecins sans frontiéres" a nata gefe ta gudanar da aiyukan bada shawarwari da gargaɗi ga mutane fiye da 56.000.

A halin halin da ake ciki, al´ummar wannan yanki na Bama, dake fama da yawan ambaliyar ruwa,da guguwa ,sun fahinci wajibcin sauraren akai akai hasashen masu ilimin sarararin samaniya.

Mawallafi: Musch-Borowska/ Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Abdullahi Tanko Bala