Bila´in jar laka mai guba a Hangari | Labarai | DW | 09.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bila´in jar laka mai guba a Hangari

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi alƙawarin ba da taimako ga Hangari domin magance bila´in malalar jar laka mai guba

default

Jar laka mai guba a Hangari

Yawan mutanen da su ka rasa rayuka a ƙasar Hangari sakamakon bila´in ambaliyar gurɓattatar laka ya ƙaru zuwa mutum bakwai.Ƙungiyar kare mahalli ta Greenpeace ta tabbatar da cewar illolin wannan ambaliya na da matuƙar barazana ga hallitu fiye da yadda hukumomin Hangari su ka ƙiyasta.A cewar Greenpeace, dalilin wannan laka mai guba akwai garuruwan da har abada ɗan adam ba zai iya sake rayuwa a cikin su ba.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi alƙawarin taimaka wa ƙasar Hangari domin hita daga wannan bila´i.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Halima Balaraba Abbas