1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

210509 Dialog Mawazine Festival

May 28, 2009

Mawazine na ɗaya daga cikin bukukuwan waƙoƙi masu muhimmanci a Marokko.

https://p.dw.com/p/Hyok
´Yan kallo wajen bikin Mawazine a RabatHoto: Maroc Cultures

Masu sha´awar kaɗe kaɗe daga duniya baki ɗaya na kwarara zuwa ƙasar Marokko inda da wuya mako guda ya wuce ba tare da an gudanar da wani bikin al´adu na ƙasa da ƙasa ba. Ɗaya daga cikin irin waɗannan bukukua shi ne bikin waƙoƙi na Mawazine wanda aka gudanar a birnin Rabat na ƙasar ta Marokko daga ranar 15 zuwa 23 ga watannan na Mayu. Bikin na Mawazine wanda aka ƙirƙiro a shekara ta 2001 na ɗaya daga cikin gangamin al´adu mafi muhimmanci a Marokko wanda ya haɗa da wasanni akan tituna, baje kolin fasahohi musamman na Larabawa da wasannin yara haɗe da na kaɗe-kaɗe.

Mawaƙa na cikin gida da na ƙetare kimanin 1700 suka hallara a birnin Rabat na ƙasar Marokko domin gudanar da bikin Mawazine karo na takwas. Daga cikin mashahuran mawaƙa da makiɗa na ƙetare da suka shiga bikin an bana har da mawaƙiyar zamani ´yar ƙasar Australiya Kylie Minogue wadda ta buɗe bikin, sai kuma Stevie Wonder ɗan ƙasar Amirka da Alicia Keys da Amadou et Mariam da Johnny Clegg daga Afirka ta Kudu da dai sauransu. Da wannan bikin Marokko ta gabatar da kanta a matsayin wata ƙasa da ta buɗe ƙofofinta ga sauran ƙasashen duniya. Sarkin Marokko Mohammed na shida wanda ke tallafawa wannan biki, na zaman wani Basarake dake ba da muhimmanci ga waƙoƙi a manufofinsa na yaɗa al´adun ƙasar.

Baya ga biranen Casablanca, Fez da Marrakesh shi ma birnin Rabat ya girgiza da kaɗe-kaɗe da waƙoƙi daga ko-ina cikin duniya. Kwanaki tara mawaƙa daga ƙasashe kimanin 40 suka nuna fasahohinsu na waƙe-waƙe a bikin na Mawazine wanda ya burge dubun dubatan maziyarta. Ko da yake biki ne na waƙoƙo, amma bisa ga dukkan alamu ya wuci wannan matsayi inji wannan mutumin da ya halarci gun bikin.

„Wannan bikin na matsayin wata shaidar cewa al´ummomi da mabiya addinai daban daban duk a haɗe suke kuma za su iya musayar ra´ayoyi game da al´adunsu. Ya kamata a san cewa kiɗa na iya ba da wannan dama. Hazalika bikin na Mawazine na kuma nuni da cewa Marokko ƙasa ce ta juriya, ƙasa ce kaɗe-kaɗe kuma ƙasa dake hannu bibiyu da kowa cikin duniya. Haka kuma bikin wani gagarumin mataki ne da Basaraken wannan ƙasa ya ɗauka musamman bisa la´akari da jagorantar wannan yekuwa da ya ke yi.“

Sarki Mohammed na shida na ba da muhimmanci wajen ɗaukaka sunan ƙasar saboda haka ne da kanshi yake jagorantar wannan biki na Mawazine wanda bana ya cika shekaru takwas. Bikin ya sake yin armashi inda aka samu jerin waɗanda suka tallafa da kuɗi domin ɗauko shahararrun mawaƙa na ƙetare zuwa Marokko. Ganin nasarar ɗauko waɗannan mashahuran mawaƙan a matsayin tallata kai ga Basaraken, amma Aziz Daki jagoran masu fasahohi na wannan bikin, ya ce sam ba haka abin ya ke.

„Wannan Basarake shi ya ƙirƙiro bikin na Mawazine. Muna cin gajiyar wannan gagarumin matakin na sa. Yana tallafa mana wajen fitowa fili da al´adu da addinai da kuma fasahohi daban daban. Bikin na Mawazine na ba da damar kare wannan matsayi.“

Wannan bikin na zaman wani shaguɓe ga masu matsanancin ra´ayin addinin Musulunci a Marokko waɗanda ba sa jin daɗin yadda ƙasarsu ke gabatar da kanta a idanun duniya. Marokko dai ba ta da wata kariya daga masu matsananci ra´ayin addini. Ko da yake an daɗe ana ɗaukar Basaraken ƙasar a matsayin shugaban ƙasa kuma jagoran addini a matsayin wani tabbaci na adawa da fassara al-Qur´ani da tsattsauran ra´ayi, amma ya rasa wannan matsayi kimanin shekaru shida da suka wuce lokacin da aka kai hare hare a birnin Casablanca inda mutane 40 suka rasu. Gwamnati dai tana ɗaukar tsauraran matakai amma shi kanshi Sarkin ya san cewa dole ya rika yin sara yana duban bakin gatari domin samun karɓuwa a tsakanin al´umarsa. Saboda haka ana iya cewa bikin na waƙoƙi na zaman wata amsa ga masu tsatsauran ra´ayi. Ko da yake a hukumance ba shi ne manufar bikin na Mawazine ba amma duk wanda ya yi habaici a kasuwa an san da wa ya ke, inji Aziz Daki.

„Al´ada da siyasa kusan ɗan Jumma ne da ɗan Jummai. Kuma haka muka ɗauki bikin na Mawazine. Duk wata al´ada da ba ta ba da damar canje-canje, kuma ba ta wata gwagwarmaya wajen wanzuwar kyakkyawar zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban daban kuma ba ta ba da damar yin haƙuri da jorewa juna to fa wannan ba al´ada ce ta gari ba.“

Hatta su kansu matasa masu matsanancin ra´ayi na goyawa sarki Mohammed na shida baya musamman game da manufofinsa na al´adu. Bigg mawaƙi ne da ke zaman na farko da fara salon waƙar Hip-Hop ciki harshen larabci a Marokko. Ya kan bayyana ra´ayinsa a cikin waƙoƙinsa, wanda miliyoyin ´yan ƙasar ke sha´awa.

„Kasancewar Basaraken wannan ƙasa ya ba da gagarumar gudunmawa, ya sa wannan bikin ya yi armashi ƙwarai da gaske. Ta haka ya taimakawa matasa waɗanda ke sha´awar waƙoƙinmu kuma ke sha´awar more rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da lumana a wannan ƙasa. Kuma muhimmin abu shi ne ya na sha´awar waƙoƙin zamani na Marokko wanda wani ɓangare ne na al´adunmu. Ganin yadda Sarkin ke mara mana baya to duk masu wa´azi na nuna ƙiyayya ba za su samu nasara ba.“

A takaice dai ana iya cewa Sarki Mohammed na shida ya na biyawa magoya bayansa buƙatunsu musamman a fannin raya al´adu da yaƙi da masu tsattsauran ra´ayin addini.

Mawallafa: Alexander Göbel/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi