1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da shari´ar birnin Nürnberg shekaru 60 da suka wuce

November 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvKF

An fara bukukuwan tunawa da zaman shari´ar birnin Nürnberg da aka yiwa tsofaffin jami´an gwamnatin ´yan NAZI shekaru 60 da suka wuce. A wannan shari´a da aka yiwa shugabannin ´ya NAZI guda 22, a karon farko cikin tarihin duniya daulolin da suka yi nasara a yakin duniya na biyu su gurfanad da mutanen da aka zarga da aikata laifukan yaki da kisan kare dangi. Daga cikin wadanda suka gurfana gaban wannan kotu har da babban hafsan soji Janar Hermann Göring da mukaddashin Hitler Rudolf Heß. An yankewa mutane 12 hukuncin kisa. A wani jawabi da yayi yau a birnin na Nürnberg sakataren kasa a ma´aikatar shari´a ta Jamus, Alfred Hartenbach yayi kira ga kasashen duniya da su amince da kotun kasa da kasa ta birnin The Hague, a wani mataki na hana aukuwar irin ta´asar da aka aikata a lokacin mulkin ´yan NAZI.