1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin sallah na hada kan Musulmi da Kirista a Najeriya

Ibrahima Yakuba/YBSeptember 12, 2016

Limaman coci-coci da sauran Kiristoci a Najeriya na shagulgulan bikin sallah tare da Musulmai domin kara karfafa dangantaka tsakanin mabiya addinai daban-daban.

https://p.dw.com/p/1K0fa
Nigeria Ramadan
Hawan sallah na zama cikin manyan abubuwa da ke kawata bukukuwan na sallahHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Yayin da Musulman duniya ke shagulgulan bikin babbar sallah a ranar Litinin din nan, limaman coci-coci da sauran manyan malaman addinin Kirista a Najeriya na taya daukacin Musulmin duniya barka da sallah tare kuma da yin kira wajan tabbatar da ganin ma su shagulgulan sallar sun taimaka wa 'yan gudun hijira da nakasassu da almajirai da mazauna kurkuku da abinci don su ma su san cewa ana bikin sallah.

Pastor Yohanna Buru da ke zaman shugaban wani babban coci a Sabon Tasha Kaduna ya bayyana ce: "Muna taya daukacin Musulmin duniya murna da zuwan wannan lokaci, kuma muna matukar fatan Allah Ya sa a kammala wannan shagulgula cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma muna janyo hankalin Musulmai da sauran alumma kasar a kan mahinmancin taimaka wa marasa karfi a wannan lokaci bisa la'akari da ganin irin matsalolin da talakawan kasa suka fada na matsin tattalin arzikin kasa".

Eid Al Fitr in Zinder, Niger
Bikin sallah ya zo a matsi na tattalin arzikiHoto: DW/L. Malam Hami

Shi kuwa Evangelist Jonathan cewa ya yi wannan lokacin murna ne ga baki daya, kuma dole ne su ziyarci Musulmai domin lokacin Kirsimeti Musulmai sun ziyarce su.

Auf der Flucht vor Boko Haram Pastor Yohanna Buru
Pastor Yohanna Buru mai fafutikar hada kai tsakanin Musulmi da Kirista a NajeriyaHoto: DW/J.-P. Scholz/A. Kriesch

Alaramma Abdulrahman Mohammad Bichi ya ce wannan shi ne zumunci, wannan abin ban sha'awa ne kuma su na yin kira ga sauran attajiran Najeriya wajen tabbatar da ganin cewa sun rika taimaka wa alumma domin kawo hadin kai da cigaba.