Bikin sake hadewar Jamus | Siyasa | DW | 03.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin sake hadewar Jamus

A yau talata ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kaddamar da bikin zagayowar ranar sake hadewar kasar

Shugabar gwamnati Angela Merkel

Shugabar gwamnati Angela Merkel

Shugabar gwamnati Angela Merkel tayi amfani da ranar bikin sake hadewar Jamus ta Gabas da ta Yamma domin waiwayar baya da kuma bitar ire-iren ci gaban da aka samu da kuma hasashen abubuwan da zasu biyo baya nan gaba. Merkel ta yi kakkausan jawabi ga kamfanonin sarrafa kayan lantarki na BenQ da Siemens tare da yin kira akan karfafa shawarwari da tuntubar juna tsakanin mabiya addinai. Ta kuma ba da misali da juyin juya halin da ya wanzu a cikin ruwan sanyi a tsofuwar Jamus ta Gabas wanda ya kai ga sake hadewar kasar Jamus karkashin tuta guda.

“Jeki ki kutsa kai ki tinkari gaba. Wannan shi ne abin da na rika ji a farko-farkon hadewar Jamus, kuma wannan shi ne abin da zan fada wa al’umar kasar a yanzun. Wajibi ne mu tashi haikan mu yi amfani da wannan dama wajen hadin kai da tabbatar da adalci. Wajibi ne mu aiwatar da dukkan kyawawan manufofinmu a karkashin wani yanayi na hadin kai da adalci da walwala.”

Kafin jawabin nata a dandalin shagulgulan bikin sake hadewar da aka gudanar a Kiel, shelkwatar jihar Schleswig-Holstein dake can kuryar arewacin Jamus, sai da gwamnan jihar kuma shugaban majalisar gwamnonin jihohin Jamus Peter Harry Carstensen yayi nuni da kyakkyawan sakamakon da aka cimma tun bayan sake hadewar Jamus shekaru 16 da suka wuce. Ya ce hatta kasashen waje na yaba wa wannan ci gaba na tarihi da Jamus ta samu.

“Al’umar gabacin Jamus sun zage dantsensu suna masu aiki tukuru tare da bada gagarumar gudummawa kuma wajibi ne a yaba musu. Su kuma ‘yan yammacin kasar sun ba da kyakkyawan hadin kai akan mnufa kuma hakan shi ma ya cancanci yabo. A ganina wannan taimakon juna da aka samu shi ne abin da ya kamata a ba wa fifiko a duk lokacin da ake batu a game da sake hadewar Jamus.”

Kimanin mutane dubu da metan suka hallara a dandalin bikin, wadanda suka hada da jami’an siyasa da ‘yan kasuwa da tsaffi da kuma shuagabannin kasashe na ketare da jami’an diplomasiyya daga sassan duniya daban-daban da kuma wakilan jihohin Jamus 16.