1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin rantsar da sabon shugaban kasar Nigeria

May 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuKR

A safiyar yau ake rantsar da Alhaji Umaru Musa Yar Aduá a matsayin sabon shugaban Nigeria. Yar Aduán mai shekaru 56 da haihuwa kuma tsohon gwamnan jihar katsina, shi aka baiwa nasara a zaɓen da ya gudana a ƙasar a watan jiya wanda masu sa ido na ƙasa da ƙasa suka baiyana cewa an tabka magudi da Almundahana a cikin sa. Tare da bujire ma kiraye kirayen sake zaɓen, sabon shugaban zai karɓi rantsuwar kama aiki a wani ƙasaitaccen biki da aka shirya a birnin tarayyar Abuja. Miƙa ragamar mulkin na zama wani babban abin tarihi a ƙasar ta Nigeria wadda ke da mafi yawan alúma a Nahiyar Afrika, kasancewar wannan shine karon farko da gwamnatin farar hula zata miƙa mulki ga wata zaɓaɓɓiyar gwamnati. Amurka da Britaniya uwargijiyar Nigeriar sun tura ƙananan jakadu su albarkanci rantsarwar wanda ake sa ran wasu yan ƙalilan daga shugabanin Afrika za su halarta. Sabon shugaban Umaru Musa Yar Aduá yayi alƙawarin cigaba da manufofin tattalin arziki na shugaba mai barin gado Olusegun Obasanjo wanda ya sami yabo daga gamaiyar ƙasa da ƙasa, amma ba tare da fidda talakawan ƙasar daga ƙangin talauci ba.