Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Jamus | Siyasa | DW | 01.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Jamus

A yau alhamis ne aka kaddamar da bikin rantsar da sabon shugaban kasar Jamus Horst Köhler dake da shekaru 61 da haifuwa

Bikin rantsar da sabon shugaban kasar Jamus Horst Köhler

Bikin rantsar da sabon shugaban kasar Jamus Horst Köhler

Sabon shugaban kasar na Jamus, kwararren masanin al’amuran tattalin arziki, wanda a yau alhamis aka yi masa mubaya’a, a hakika mutane a nan kasar ba su san shi ba a lokacin da ‚yan Christian Union da FDP suka zabe shi domin shiga takarar neman wannan mukami. Amma jawabinsa na farko da ya gabatar ba shakka zai taimaka illahirin Jamusawa su mayar da hankali domin ganin salon kamun ludayinsa. Kafin dai a gabatar da bikin ba mubaya’a, sai da aka fara gudanar da shagulgulan ban-kwana ga magabacinsa Johannes Rau, wanda a cikin jawabinsa yayi kira ga jama’a ga nuna hadin kai musamman a daidai wannan lokacin da ake fama da mawuyacin hali, inda ya kara da cewar:

Kasar nan ta dogara ne kacokam akan kwazo da hazakar da Allah Ya fuwace wa al’umarta. Kazalika da kauna da hadin kai da ‚yan-uwantaka tsakaninsu. Babbar matsalar da wajibi ne a shawo kanta ita ce ta rashin aikin yi da ta zame wa al'umarta kayar kifi a wuya. Amma abu mafi muni shi ne yadda akan wayi gari an mayar da mutane saniyar ware a harkokin rayuwa ta yau da kullum.

A ranar 23 ga watan mayun da ya wuce ne Horst Köhler dan takarar jam’iyyun Christian Union da FDP ya cimma nasarar kuri’ar raba gardamar da majalisar hadin guiwa ta majalisun jihohi da ta dokoki ta kada, inda ya samu goyan baya na wakilai 604 daga cikin wakilan majalisar su 1204. Tun a wancan lokaci ya fito fili ya bayyana alkiblar da zai fuskanta, inda ya ce zai tsoma bakinsa a matsalolin dake addabar Jamus da kuma matsin kaimi wajen ganin an magance su. Ya ce wajibi ne a tashi tsaye wajen magance wadannan matsaloli ba tare da wani jinkiri ba. Ya yaba da matakan garambawul da gwamnati ta gabatar dangane da tsarin kyautata jin dadin rayuwar jama’a da makomar kasuwar kodago. To sai dai kuma abin bacin rai shi ne matakai na hana ruwa gudu da ake fuskanta tsakanin gwamnati dake da rinjaye a majalisar dokoki ta Bundestag da ‚yan hamayya na Christian Union dake da rinjaye a majalisun jihohin Jamus. Köhler ya kara da bayani yana mai cewar:

A saboda haka nike yin kira ga sassan biyu da su yi watsi da banbance-banbancen dake tsakaninsu dangane da zabubbukan da za a fuskanta a wannan shekarar ta yadda a karshe zata zama shekara mai albarka ga kowa da kowa. A shekarun baya mun gaza wajen daukar nagartattun matakai da suka dace domin sabunta tsarin zamantakewar jama’a a nan kasar tare da ba da la’akari da canje-canjen da ake samu a rayuwa ta yau da kullum.

Bisa ga ra’ayin sabon shugaban na Jamus dai wajibi ne a tashi tsaye a tinkari matsaloli masu tarin yawa dake addabar kasar a maimakon korafi da maganganu na fatar baki kawai. A yanzun ba abin da ya rage illa a sa ido a ga salon kamun ludayinsa.