1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin rantsar da sabon babban alkalin Najeriya

March 7, 2017

An rantsar da sabon babban alkalin Walter Samuel Nkanu Onnoghen cikin wani yanayin jayayyar fasalin da yakamaci yakin da cin hancin a kasar ya dauka yanzu.

https://p.dw.com/p/2Ympp
Samuel Nkanu Onnoghen daga dama sanye da tuta a jikinsa,Yemi Osinbajo mataimakin shugaban Najeriya daga hagu
Samuel Nkanu Onnoghen daga dama sanye da tuta a jikinsa,Yemi Osinbajo mataimakin shugaban Najeriya daga haguHoto: Ubale Musa

Samuel Nkanu Onnoghen da ke zaman alkali na 20 da zai jagoranci bangaren shari'ar kasar dai na shan rantsuwa ta kama aikin ne a cikin yanayin rudani a tsakanin bangaren zartarwar da ke zargin alkalai na kasar da dakile yakin da cin hanci, da kuma alkalan da ke zargin masu yin mulkin da kokari na wucce makadi da rawa a cikin tsarin.Tun da farko da ba a boye yake ba,shugaban rikon kasar  Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi sauyi a cikin tsarin sharii'ar na kasar.

Samuel Nkanu Onnoghen  sabon babban alkalin Najeriya
Samuel Nkanu Onnoghen sabon babban alkalin NajeriyaHoto: Ubale Musa

Wannan lamari na zuwa ne a  lokacin da dukkanin bangarorin na gwamnati ke fuskantar matsalar dawowa daga rakiyarsu a bangare na kasar,har ma da tsarin shari'a.To sai dai sabon babban alkalin ya sha alwashin maido da kima da kuma darajar akalan a idon al'ummar Najeriya wadanda suka dade da yin watsi da lamarin shari'a a kasar saboda yawan cin hancin da ake samu a cikin batun.Abin jira a gani dai na zaman mataki na gaba a tsakanin alkalai na kasar  da ke da karfin ikon kai wa ya zuwa nasarar yaki da cin hancin da kuma bangare na zartarwar da ke fadin dole alkalain su hau sahu.