1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin nuna zumunci ga kananan yara da ake tilasta musu shiga aikin soji

Mohammad Nasiru AwalFebruary 14, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlt
An dai sha tambayar Senait Mehari ko zata iya yin bayani dalla-dalla game da halin da ta taba samun kanta a ciki? Masu yi mata wannan tambayar dai na mamakin yadda aka yi Senait ta shiga aikin soji sanda take yarinya ´yar shekara 6 da haihuwa, har ma ta fafata a lokacin yakin basasan Eritrea. Amsar da take bayarwa dai ta shafi gwagwarmayar da suka sha ne a bakin daga. Senait da iyayen ta sun yi kaura zuwa nan Jamus, kuma yanzu haka ta cika shekaru 27 da haihuwa kana kuma ta zama shahararriyar mawakiyar kidan pop. Tana daya daga cikin mawakan da aka gayyace su a wannan biki na nuna zumunci ga kananan yara da ake tilasta musu shiga aikin soji. Wannan dai ba shine karon farko da yaran makaranta a nan Jamus suka gudanar da irin wannan biki tare da yin jerin gwano kan tituna don tunawa da takwarorinsu da ake tilasta musu daukar makami a yankunan da ake fama da yake-yake ba. A lokacin yakin Iraqi a bara, dubun dubatan yaran makaranta sun gudanar da zanga-zanga da tarukan gangami don nuna adawa da wannan yaki. Duk da cewa kudurin kare hakin kananan yara ya haramta daukar yaro da shekarunsa na haihuwa ba su kai 18 aikin soji ba, amma alkalumma sun yi nuni da cewa akwai kananan yara kimanin dubu 300 da ake tilasta musu shiga aikin soji a duk fadin duniya. Da yawa daga cikinsu kuwa ana cin zarafinsu tare da take musu hakinsu. Ya zuwa yanzu ba´a san yawan kananan yara da ke mutuwa a kullu-yaumin a bakin daga ba. To amma kadan daga cikinsu da Allah yayiwa gyadar dogo suka tsira da rayukansu kamar Senait Mehari, zasu dade ba su manta da irin mawuyacin hali da suka shiga ciki da kuma abubuwa na ban tsoro da suka gani a lokacin wannan gwagwarmaya da suka sha ba.