1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin mabiya addinin Hindu

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 3, 2007

Miliyoyin mabiya addin Hindu ne suka fara tsunduma cikin kogin ganges a arewacin Indiya,suna masu fatar wanke kansu daga zunubbansu tare da fatar samu dauwammamiyar rayuwa.

https://p.dw.com/p/Btwn
Kogin Ganges
Kogin GangesHoto: AP

Daruruwan waliyan addinin addinin hindu ne tsirara sunshafe jikunansu da toka,sun cakudu da miliyoyin jamaa da suke je wannan wanka suna sanya masu albarka a magamar kogin Ganges da yamuna a garin Allahbad.

Akalla mutane miliyan 50 ne ake sa ran zasuyi wanka cikin wannan kogi a kawanki 45 na wannan buki,wanda ake gudanarwa bayan kowane shekaru 6.

Babban sakataren jihar Uttar Pradesh C.Bajpai yace ya zuwa yanzu akalla mutane miliyan 2.5 sun isa wurin tuni kuma fiye da rabbinsu sun rigaya sunyi nasu wanka.

Yara da manya da tsoffi mabiya addainin na Hindu dama baki yan kasashen waje dake son ganewa idanunsu wannan biki.

Mr.Bhattacharya ya fito ne daga wannan yankin yace mabiya addinin na Hindu sun dauki wannan bikin da muhimmanci kuma yana da muhimmanci ganin cewa yazo dab da kammala aikin hajji na musulmi.

cikin miliyoyin mutane dake wajen bikin akwai yan sanda kusan 50,000 donmin tsaro,wani babban jamiin yankin ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AFP cewa, sun samu rahotannin yiwuwar kai harin taadanci a lokacin wannan biki,saboda haka wasu yan sandan ciki zasu kasance tsirara kamar waliyan Hindu domin su saje da jamaa su kuma gano yan taaddan.

Mabiya dariku na Hindu daban daban suna rike da tutocin darikunsu suna kuma watsi da tsananin sanyi da kogin yayi suna ci gaba da wankan su kamar yadda addininsu ya bukata.

Mr Bhattacharya na sashen Hindu yace wannan biki dai na wanaka a kogin ba tilas ne akan mabiya Hindu suyi ba.

Domin kare yamutsi an kafa kofa daya ta shiga harabar kogin yayinda kuma aka samarda kofofi guda uku na fita daga yankin.

Akwai kuma wani biki babba nan gaba wanda ake gudanarwa bayan shekaru 12 a wannan kogin na Ganges.