Bikin Karneval ya guji duk abin da zai shafi zanen nan na ɓatanci. | Zamantakewa | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bikin Karneval ya guji duk abin da zai shafi zanen nan na ɓatanci.

Bikin Karneval dai, biki ne da ake yi a ko wace shekara a nan Jamus. Asalinsa na da jiɓinta ne da mutanen da, waɗanda suka yi imanin cewa, akwai iskoki waɗanda ya kamata su kora kafin farawar bazara. To a halin yanzu kuwa, barkwanci ake yi a lokacin bikin, a kan `yan siyasa da wasu halaye na zaman jama'a. Masu shirya bikin dai sun ce, ko kaɗan ba za su taɓo batun zanen ɓatancin nan da ya ta da hankalin musulmi a duk duniya baki ɗaya ba.

Bikin Karneval a birnin Kolon.

Bikin Karneval a birnin Kolon.

Bikin Carneval ana yinsa ne don shaƙatawar jama’a. A lokacin bikin, sai ka ga duk titunan manyan birane sun cika maƙil da mutane da kuma manyan motoci da aka yi wa ado, wasu mutanen kuma na cikinsu suna ta kaɗe-kaɗe da raye-raye, suna ta jefa wa jama’a a gefen titi furanni da alawa da sauran kayan zaƙi.

A lokacin wannan bikin ne kuma, bisa al’ada, ake zaɓan barkwanawa waɗanda ake kira die „Jecken“, don su yi barkwanci da `yan siyasa, su yi ta ababan ban dariya game da su. Sau da yawa a kan ɗora mutum mutumin wani shahararren ɗan siyasa a kan motocin da ke wucewa kan titi, wanda kuma a kansa ne za a yi barkwancin. Akwai dai jigogi da dama da aka zaɓa waɗanda za a yi wasannin kwaikwayo na ban dariya a kansu. Sai dai, an yi taka tsantsan, ba a taɓo batun nan na ɓatancin da aka yi wa musulmi ba, wanda aka yi ta ƙorafi a kansa a duniya baki ɗaya. Harad Schmidt, wani babarkwane, mai wasan kwaikwayo a kan talabijin, wanda kuma shi ne zai jagoranci jerin gwanon bikin wannan shekarar a birnin Düsseldorf, ya bayyana dalilin da ya sa aka kauce wa takalo batun ɓatancin a bikin:-

„Ko kaɗan, ba za mu faranta wa shaiɗan rai ba. Yin kwaikwayo da zanen ɓatancin ai wulakanci ne ga wasu, kuma mummunar ɗabi’a ce. Ai ma ba abin ban dariya ba ne. Ni dai ko da an yi ma, ba zai sani dariya ba. Bai kamata kuma mu ƙara wa wuta kanazir ba. Duk abin da har ya janyo asarar rayuka, to ba abu ne na ban dariya ba. Bai kamata dai a ce mu ɓata wa wasu ransu yayin shaƙatawarmu ba. Fiye da mutane `yan kallo miliyan ɗaya ne za su kasance a nan Düsseldorf. Burinmu ne mu ƙayatad da kowa mu sa su dariya.“

Harald Schmidt, ya ƙara bayyana cewa, duk da kwaikwayon ababan da suka shafi siyasa da za a yi a wannan bikin, ko kaɗan ba za a takalo batun zanen ɓatancin ba.

A birnin Kwalan ma, ɗaya daga cikin manyan biranen da suka yi tashe wajen gudanad da bikin Carneval ɗin a nan Jamus, an ƙaurace wa wannan jigon. Za yi dai barkwanci ne kan jigon wasan ƙwallon ƙafa, ta yin la’akari da karaɓar baƙwancin wasannin cin kofin duniya na ƙwallon ƙafar da za a yi a nan Jamsu a cikin wannan shekarar. Siegfried Krebs, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar Carneval ɗin ta birnin Kwalan, ya bayyana cewa a barkwanawan birnin ma za su takalo batutuwan da suka shafi siyasa, amma su ma, an yi musu gargaɗi da su guji duk wani kwaikwayo da zanen ɓatancin. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Bikin Carneval ɗin Kwalan ba shi ba burin tayar wa mutane hankullansu, musamman game da abin da ya shafi addinansu. Ko kaɗan ba za mu shiga cikin wannan salon ba. Wannan halin ba ya cikin aƙidarmu a nan Kwalan. ..Ba burinmu ba ne mu nuna wulakanci ga jama’a ko kuma addinansu da al’adunsu.“

Duk dai shugabannin ƙungiyoyi daban-daban na Carneval din sun ce bikin da kansa na da asali ne daga al’adun mutanen da. A nan jihar ta Rheinland, bisa al’ada, wato biki ne da mutane ke yi don shaƙatawa, kafin fara azuminsu a lokacin ista, ga mabiya addinin kirista. Da can kuma kafin zuwan addinin kiristan ma, ana wannan bikin ne a galibi a kudancin Jamus don korar miyagun iskoki kafin shiga lokacin bazara. To tun da daɗewa dai, haka ake wannan bikin.