Bikin karbar karin membobin majalisar turai | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin karbar karin membobin majalisar turai

A yau ne akayi bikin karbar kasashen Bulgaria da Romania cikin majalisar turai a birnin Strasbourg.

Yanzu haka shigar wakilan Romania 35 da kuma na Bulgaria 18,membobin majalisar turai tana da membobi 785.

Karbar kasashen biyu cikin kungiyar ya baiwa jamiyu masu sassucin raayi daga kasashen turai samun kujeru a majalisar ta turai tare da samun daukar nauyin jamiyunsu,wadanda tun farko suke adawa da shigar kasashen Romania da Bulgaria cikin kungiyar.