Bikin gidajen tarihi a duniya
May 21, 2009Talla
A ranar 18 ga watan Mayu aka gudanar da bikin ranar gidajen tarihi na duniya. Ana gudanar da wannan biki ne domin jawo hankalin jama´a game da muhimmancin adana kayakin tarihi da na al´dun gargajiya don amfani jama´a. Ita ma jihar Kaduna a Najeriya ta bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen gudanar da wannan biki, inda baya ga kaɗe kaɗe da raye raye an kuma gabatar da jawabai kan matsayin gidajen tarihi tare da yin kira ga shugabannin da su taimakawa wajen haɓaka waɗannan gidaje na adana kayakin tarihi.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi