1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin Gabatar Da Kwamitin Tsaro Na Kasashen Afurka

May 25, 2004

A yau talata ne aka gabatar da bikin kama aikin kwamitin tsaro da zaman lafiyar Afurka a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha

https://p.dw.com/p/BvjL
Bikin kafa Kungiyar Tarayyar Afurka
Bikin kafa Kungiyar Tarayyar AfurkaHoto: AP

A hakika dai ba wanda ya taba tunanin cewar kasashen Afurka dake fama da tafiyar hawainiya ga manufofinsu zasu dauki wani mataki na kafa wani kwamitin tsaro da zaman lafiya a wannan nahiya irin shigen kungiyar nan ta tsaro da hadin kai a nahiyar Turai OSCE a takaice, wacce kasashen nahiyar suka kirkiro a cikin shekarun 1970. Wani azanci da kasashen Afurka suka yi a game da wannan ci gaba shi ne yadda suka danganta taken kwamitin nasu da na MDD duk kuwa da cewar suna masu koyan darasi ne daga ire-iren matsalolin da kasashen Turai suka fuskanta a zamanin yakin cacar-baka tsakanin kasashen gabaci da na yammacin nahiyar. Kasashen Afurka ba sa sako-sako da duk wani abin da zai zama alheri a garesu. Kuma wannan kwamitin wani mataki ne da ya cancanci yabo da guda. Bugu da kari kuma zai samar musu da taimakon kudi idan har sun dauki maganar tsaro da kiyaye zaman lafiya da riga-kafin rikice-rikice da muhimmanci. A dai wannan marra da ake ciki yanzu, murna na neman komawa ciki dangane da ci gaban da kasashen nahiyar ke samu a fannin mulki na demokradiyya, sakamakon rikice-rikice da suka zama ruwan dare a wasu sassa na Afurka. Wajibi ne akan masu mulki a kasashen nahiyar su nemi bakin zaren wadannan rikice-rikice domin cimma kwanciyar hankali da daidaituwar al'amuran siyasa. Kafa wannan kwamiti na tsaro da aka yi, kazalika, abu ne dake bayyanarwa a fili cewar kasashen Afurka a shirye suke su janye daga wani bangare na ikon cin gashin kansu don amfanin kowa-da-kowa. Duk wanda ya ba da la’akari da maganar kafa rundunar kwantar da tarzoma bai daya tsakanin kasashen Afurka da kuma ba wa wakilan hukumar kare hakkin dan-Adam ta Afurka wata dama tofa albarkacin bakinsu a ayyukan kwamitin na tsaro da zaman lafiya zai samu kwarin guiwa a game da kyakkyawar niyyar dake akwai na shawo kan matsalolin nahiyar Afurka. Gaba daya kirkiro wannan kwamiti da aka yi babban ci gaba ne da ya kamata a yi marhabin da shi a kuma lura da cewar lokaci yayi da za’a ba wa Afurka kyakkwan matsayin da ya dace da ita a siyasar duniya, domin ta haka ne kawai kasashenta zasu samu kwarin guiwar tinkarar dukkan matsalolin da ake addabarsu su kuma nemi bakin zaren warwaresu.