1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin furannin bishiyar Cherry a birnin Bonn

Aisha Bello Mahmoud/ BSApril 27, 2016

Bikin furanni na itaciyar Cherry ana yin shi ne daga shekara zuwa shekara a birnin Bonn, kuma ya sha bambam da sauran bukukuwa da ake gudanarwa.

https://p.dw.com/p/1IdmN
Kirschblütenfest Bonn
Hoto: DW/Y. Ibrahim

'Yan yawan bude ido ne ke turuwar zuwa don gane wa idanuwansu irin yadda itaciyar ta kawata daya daga titunan birnin Bonn kamin hudar furen na Cherry ya bace bayan kwanaki kalilan. Yayin bikin an gudanar da kade-kade a wasu tituna na unguwar Altstadt da ke a birnin na Bonn, inda ake gudanar da wannan bikin a farkon rani na kowace shekara, a kan babban layin da ya bi ta wannan unguwa wanda ya shiga jerin wurare mafiya kyau da ke fadin duniyar nan. Duk wani mahaluki dai zai so ya yi tozali da wannan titi musamman ma a yayin da furanni na Cherry masu launin ruwan hoda suka fito, inda suke wa titin rumfa kuma suna daukar ido. Wani matashi da ya halarci wurin har ma ya dauki hutunan wadannan furanni cewa ya yi.

Bijit aus Indien
Bijit wani dan kasar Indiya da ya halarci bikin furannin Cherry a BonnHoto: DW/Y. Ibrahim

"Ni ne Bijit na zo ne daga Indiya don ingane wa idona. Bayan na samu labari a wurin abokaina sai na kudiri aniyar cewa lallai ya kamata na zo don ina da burin kara ilimi a kullum. Hakika wannan titi yana da kyau da ban sha'awa. Kuma an ce furen iyakarsa mako uku kawai zai fito a shekara, don haka a wurina sai in ce wajibi ne mutum ya zo ya gane wa idanunsa."

Wandannan furanni na Cherry suna jere ne reras a dama da hagun na wannan layi, inda suke mai da titin na unguwar ta Altstadt wani wuri mai kyalli musamman ma idan rana ta haska, don haka masu yawon bude ido da mutanen gari ke dafifi a wurin. Wasu mahalarta bikin sun bayyana ra'ayin su dangane da yadda suka ga bikin na bana.

"Ann sunana, hakika na ji dadi matuka da na zo nan duk da dai rana ba ta fito ba ina ganin in rana ta fito abikin zai fi kyau. Sai dai kuma akwai mutane da yawa sai ka yi da gaske za ka wuce amma dai hakan abu ne mai kyau"

"Kusan shekara 10 ko 15 aka fara wannan biki, inda ake gudanar da shi a kwanaki biyu na karshen mako. Abin sha'awa furannin suna kurkusa da junansu kuma suna da kyawon launi na ruwan hoda mai daukar hankali. Sai dai mutanen Asiya su ne suka fi halartar wannan taro, ban cika ganin 'yan yankin Afirka a wanann biki ba."

Claudia aus Bonn
Claudia daga birnin Bonn yayin hira da wakiliyar DW Aishatu Bello MahmudHoto: DW/Y. Ibrahim

"Sunana Claudia, wannan shi ne karo na farko da na halarci wannan biki. Ina zaune a nan Bonn kusan shekaru uku kenan kuma tun sannan na san ana yin wannan biki."

Baya ga 'yan yawan bude ido, akwai masu zuwa daga wasu wurare a ciki da wajen Jamus don cin kasuwar wannan biki na furannin na Bonn, kamar yadda wani da ke saida kayan da aka sassaka yake cewa...

"Daga birnin Koblenz na taho, kuma a gaskiya yadda mutane suka cika haka daga ko ina a fadin duniya yanayi ne mai kyau. Ina fatan zai bunkasa kasuwanci da al'ada, don wannan biki wani abu ne da ke hada kan al'ummar duniya kuma duk wanda ya zo ya ga yadda bishiyoyin na Cherry suka bude furanninsu yana da matukar kayatarwa."

Duk da cewa a kan yi irin wannan biki a birane kamar su Washington na kasar Amirka da wasu kasashe na yankin Asiya, amma babu wanda ya kai na unguwar Altstadt da ke birnin Bonn a nan kasar Jamus kyau da shahara, duba da yadda itaciyar ta Cherry ke kawata wannan hanya a makwanni uku na kowace shekara ko kuma kasa da haka.