Bikin Fespaco | Siyasa | DW | 25.02.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin Fespaco

A na ci gaba da shagulgulan Fespaco karo na 20 a birnin Ouagadougou

default

A Ouagadougou babban birnin Burkina Faso, a na ci gaba da gasar nuna fina finai, da shirye-shiryen Talbajan na ƙasashen Afrika, da aka fi sani da suna Fespaco.

Ranar asabar da ta wuce ne, shugaba Blaise Comapaore, tare da sakatare Janar, na ƙungiyar ƙasashe masu anfani da halshen Faransanci Abdu Diouf, su ka jagorancin shaggulgulan buɗa wannan biki da ke gudana , duk ko wace shekara 2, a birnin Ouagadougou da ke matsayin cibiyar harakokin Silma a nahiyar Afrika.

A bana, za a gabatar da fina-finan sama da ɗari 2 wanda Afrikawa na cikin gida da ƙetare su ka shirya.

Babban jami´i mai kulla da wassani Fespaco, Baba Hama, ya nunar da inganci wannan fina-finai ta fannin al´adu da tarbiya Afrikawa, sannan ya ce ya zama wajibi a tashe tsaye sanar da dunia albarkatun fina-finai da Afrika ta kunsa.

„ Idan Afrika ta yi kwance da kaya,cikin wannan yanayi, wanda dunia ta kasance tamkar wani ɗan ƙaramin gari,inda kowa ya san kowa, kuma cudayar al´adu ke gaba da haɓɓaka, to za mu kasance kullum a matsayin yan kallo.

Ya zama wajibi mu tashi tsaye mu yada al´adun mu, ta hanayar anfani da fina finai.

Yadda al´ummomin Afrika, ke maida hankali wajen kalon fina-finan da su ka zo daga ƙetare, kamata tayi muma mu yaɗa na mu fina-finan a san su a dunia.

Saidai ba za a cimma wannan buri ba, saidai cikkaken goyan baya daga magabata“.

A lokacin da aka ƙaddamar da bukin fara gasar, an nuna fina finai guda 3 ,da su ka haɗa da 2 na Mali, da kuma ɗaya na Tunisia.

A wannan karo wanda shine na 20 da aka fara gasar Fespaco an tanadi karamci na mussaman ga finan- finan ƙƘasar Mali ta la´akari da ci gaban da ake samu, a wannan ƙasa ta wannan fanni.

Za a cigaba da gudanar da bikin har ranar 3 ga watan Maris mai kamawa.

 • Kwanan wata 25.02.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btw6
 • Kwanan wata 25.02.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btw6