Bikin fara aikin yarjejeniyar Kyoto | Siyasa | DW | 17.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin fara aikin yarjejeniyar Kyoto

A jiya laraba ne hukumar MDD mai kula da makomar yanayi dake da hedkwatarta a nan Bonn ta gabatar da bikin kama aikin yarjejeniyar kayyade dimamar yanayin duniya ta Kyoto

An samu gabatar da aikin yarjejeniyar ne bayan da kasar Rasha ta albarkaceta bayan daridari da tayi da lamarin da farkon fari, ko da yake Amurka har yau tana ci gaba da nuna taurin kai duk da cewar ta fi kowace kasa fitar da wannan hayaki mai guba dake haddasa dimamar yanayin duniya. A jiya laraba, hukumar MDD akan manufofin kare yanayi dake da shelkwatarta a nan birnin Bonn ta gabatar da bikin kaddamar da aikin yarjejeniyar ta Kyoto tare da halarcin ministan muhalli na Jamus Jürgen Trittin. An samu daidaituwar baki tsakanin wakilan gwamnati da na kungiyoyin kare kewayen dan-Adam da kuma na wani kamfanin mai wajen bayyana farin cikinsu da fara aikin wannan yarjejeniya. A lokacin da yake bayani Jürgen Cuno, wakilin kamfanin mai na BP bangaren Jamus nuni yayi da cewar:

Kamfanin BP na tattare da imanin cewar wajibi ne akansa ya bada gudummawa iya mustada’a a matakan kare makomar yanayin duniya. Domin ta haka ne kawai za a iya kwantarwa masu hannayyyen jari na kamfanin hankalinsu. Wannan wata babbar dama ce da za a iya kwatanta ta tamkar dai faduwa ce ta zo daidai da zama. Domin tana ma’anar canjin manufofi ne ga al’umar kasa da kuma ‚yan kasuwa, ta yadda wani sabon abu zai iya billa, kamar yadda aka saba gani a ire-iren wadannan canje-canje a zamanin baya.

Shi ma ministan kare muhalli na Jamus Jürgen Trittin sai da yayi tsokaci da gaskiyar cewa matsalar dimamar yanayin matsala ce da ta samu tuntuni, ba wani lamari ne da ake hasashen afukuwarsa ba. Yayi wannan bayani ne ganin yadda wasu ke korafin cewar matakan kare makomar yanayin suna cin makudan kudi. Ya ce asarar da zata biyo baya, in har an kuskura an yi fatali da wannan manufa, to kuwa zata fi tsada. Jürgen Trittin ya bayyana alfaharinsa a game da rawar da Jamus ta taka wajen kayyade yawan hayakin carbon-dioxid da take fitarwa zuwa sararin samaniya, bisa sabanin kasar Amurka wacce yawan abin da take fitarwa ya ninka na kasashen Turai har sau biyu. To sai dai kuma wannan ci gaban da Jamus ta samu ya zo ne sakamakon rushe wasu tsaffin kamfanonin da aka yi a tsofuwar Jamus ta Gabas, amma a wannan marra da ake ciki yanzu ana fama da tafiyar hawainiya, inda a shekara ta 2000 ma aka samu karuwar yawan hayakin na carbon-dioxid da kamfanonin kasar ke fitarwa zuwa sararin samaniya.