1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin cika shekaru 60 da shari´ar birnin Nürnberg

Wannan shari´ar ta kasance tushen shari´ar da ake yi wa wadanda ke aikata laifukan yaki a duniya baki daya a wannan zamanin da muke ciki.

Shari´ar masu aikata laifukan yaki a Nürnberg a 1945

Shari´ar masu aikata laifukan yaki a Nürnberg a 1945

Tun a lokacin yakin duniya na biyu ya tabbata cewa shugabannin kasashen kawance zasu gurfanad da ´yan Nazi a gaban kotu. To amma kashe kansu da Hitler da Himmler da kuma Goebbels suka yi ya sa ba´a iya daukar wannan mataki kansu ba. To sai sai dai sojojin Amirka sun cafke Hermann Göring, ministan sufuran jiragen sama kuma a jefi-jefi na hannun damar Hitler lokacin da ya so tserewa da iyalinsa a cikin manyan motoci 17 cike da kayayyaki. Tashar BBC a wancan lokaci ta rawaito kamun sa kamar haka.

“Göring na sanye da da unifom masu aninai na gwal na bataliya ta Hermann Göringa da aka sanya mata sunansa.”

Göring dai shine jami´in gwamnatin ´yan Nazi mafi girma a lokacin da alkalin TS Nikitschenko ya bude zaman sauraron shari´ar a ranar 20 ga watan nuwamban shekarar 1945 a birnin Nürnberg. Mutane 21 ne suka gurfana gaban kotu a wannan rana. Dukkan su an tuhume su da aikata laifuka 4, na farko ta da fitina na biyu shiryawa da haddasa tare da kaddamar da wani yaki na babu gaira. Na 3 shine aikata laifukan yaki da karya dokokin yaki sai na 4 shine aikata laifi akan ´yan Adam. Göring dai bai amsa laifin da aka zarge shi da aikatawa ba.

“Ban shirya ko kuma kaddamar da wani yaki ba. Na yi duk iya kokarin hana haka aukuwa ta hanyar yin sulhu.”

Lauyoyin su dai sun yi zargin cewa shari´ar ba ta kan doka illa iyaka ta dogara ne akan wasu dokoki da aka kirkiro bayan an aikata wadannan laifuka. To amma shugaban alkalai kuma dan Birtaniya Sir Geoffrey Lawrence yayi watsi da wannan zargi yana mai cewa ai Jamus ma ta amince da dokokin kasashen duniya da suka tanadi yin amfani da hanyoyin lumana wajen warware rikici tsakanin kasashe.

Daga cikin wadanda aka yiwa shari´ar akwai Hans Frank tsohon gwamnan yankin Poland da ´yan Nazi suka mamaye. An tuhume shi ne da kisan ´yan siyasa da masu ilimi na Poland sai yiwa Yahudawa kisan kare dangi tare da tilastawa ´yan Poland yin kwadagon tilas a masana´antun kera makamai na Jamus.

Shi kuwa Göring wanda a wasu lokutan ya kasance na hannun damar Hitler ya ce ba ruwansa da kisan kiyashin da aka aikata.

“Ba da wata rufa-rufa ba ina mai yin Allah wadai da wannan mummunan kisan kare dangi, wanda daidai da rana daya ban taba amincewa da shi ba.”

An kammala gabatar da shaida bayan kwanaki 72 na zaman kotun. Amma lauyoyi da kuma wadanda aka gurfanar ba su amsa laifin sun ba. Göring cewa yayi so da kauna da yake yiwa kasar sa da kuma al´umarta suka angiza shi.

A karshe dai wato a ranakun 30 ga watan satumba da daya ga watan oktoba kotun ta same su da aikata dukkan laifukan guda hudu, inda ta yankewa mutane 12 hukuncin kisa ta hanya ratayawa, 7 hukuncin dauri a gidajen yari sannan 4 aka sallame su. To amma a ranar 16 ga watan oktoban shekarar 1946 sa´o´i kalilan gabanin aiwatar da hukuncin kotun Göring ya kashe kansa ta hanyar shan guba. Ba kamar yadda aka tsara da farko ba, daga baya an dakatar da yin shari´ar a wata kotun soji ta hadin guiwa tsakanin daulolin da suka yi nasara a yakin duniya na biyu. To amma yau shekaru 60 bayan wannan shari´a akwai kotunan MDD da ke shari´ar masu aikata laifukan yaki kamar ta birnin The Hague dake shari´ar wadanda suka aikata ta´asar yaki a tsohuwar tarayyar Yugoslabiya da ta birnin Arushan Tanzaniya mai zaman sauraron shari´ar da ake yiwa wadanda suka aikata kisan kiyashi a Rwanda.

 • Kwanan wata 20.11.2005
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu46
 • Kwanan wata 20.11.2005
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu46