1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin cika shekaru 60 da saukar sojojin kawance a yankin Provence na kudancin Faransa

Mohammad Nasiru awalAugust 16, 2004
https://p.dw.com/p/BvhI

Lokacin da sojoji dubu 300 rabi a cikinsu daga Afirka suka isa gabar tekun Cote d´Azur cikin kananan jiragen ruwan yaki yau kimanin shekaru 60 da suka wuce. Har yanzu kuwa akwai irin wannan jirgin ruwa mai kama da akwatin karfe a kusa da Dramonts, inda tsofaffin sojojin suka hadu a jiya. Wannan ziyarar ta kasance tamkar ta ibada ga Ayoun Mbaye mai shekaru 83 a duniya, wanda ya ce yana sha´awar sake ganin wannan wuri da kuma jirgin ruwa kafin ta Allah ta kasance akanshi. To sai dai yanayin wurin ya canza masa, domin yau shekaru 60 kenan da suka sauka a gabar tekun.

Shi dai Ayoun Mbaye dan kasar Senegal ne, kuma yana da shekaru 23 lokacin da aka dauke shi aikin soji a wani kauye mai nisan gaske da birnin Dakar. Yana cikin ´yan Afirka dubu 180 da aka dauke su aikin soji a karkashin wani aiki da aka yiwa lakani da ´yantarwa.

"A garemu wannan aikin tamkar farilla ne, mun hada karfi da Faransawa don mu yaki sojojin Jamus. Domin bayan ta mamaye Faransa, da Afirka ce zata zama ta biyu."

Wadannan sojojin daga Afirka sun taka muhimmkiyar rawa wajen sake ´yantad da Faransa. Saboda haka ya zama wajibi Faransa ta gode musu, inji Mbaye.

Shi kuwa a nasa bangaren Diallo Amoudou Hassan, wanda ya sake haduwa da tsofaffin abokanensa daga Nijer cewa yayi.

"Ko shakka babu mu din nan da ake kira sojojin kariya daga Senegal, mu muka sadaukar da rayukanmu don ´yantad da Faransa, ba tare da nuna son kai ba."

Wai shin Faransa zata kyautatawa wadannan tsofaffin sojojin daga kasashen da suka taba zama karkashin mulkin mallakarta? An dai shafe shekaru 40 ba´a samu wani canji ba ga kudin fansho da ake ba tsofaffin sojin. A saboda da haka yanzu suke kara matsawa ma´aikatar tsaron Faransa lamba.

"Har yanzu muna daukar kanmu a matsayin Faransawa. Saboda haka muke fatan cewa Faransa zata yi iya kokarin kara mana kudin fansho. Dole ne kuma a ba iyalanmu isasshen kudin tafiyar da rayuwarsu."

Ko da yake gwamnatin Faransa ta tsayar da shawarar kara kudin fansho amma ga malam Diallo Hassan, hakan bai wadatar ba. Sau 3 a shejara ana ba shi Euro 320, kwatankwacin kashi daya cikin 10 kenan na abin da ake ba takwaransa na Faransa. Hassan ya baiyana hakan da cewa rashin adalci ne, amma shugaba Jacques Chirac bai yarda da haka ba. A jawabin da yayi shugaba Chirac yabawa yayi ga jarumtakar da tsofaffin sojoji suka nuna, inda ya ce har abada Faransa ba zata taba mantawa da su ba.