1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin cika shekaru 30 da kisan gillar Soweto

YAHAYA AHMEDJune 16, 2006

Shekaru 30 sun wuce, tun da aka yi mummunar kisan gillar nan ga yaran makaranta da matasa a garin Soweto na Afirka Ta Kudu. A ran 16 ga watan Yunin 1976 ne, 'yan sandan gwamnatin mulkin wariya ta Afirka Ta Kudun, suka buɗe wa matasa masu zanga-zanga ta hannuka mai sanda, don nuna adawa ga yin amfani da harshen Afrikaans wajen koyarwa a makarantunsu, wuta, inda suka kashe da yawa daga cikinsu.

https://p.dw.com/p/Btzh
Unguwar marasa galihu a garin Soweto
Unguwar marasa galihu a garin SowetoHoto: Das Fotoarchiv

A wannan lokacin dai, shahararriya mai waƙar nan ta Afirka Ta Kudu, Miriam Makeba, na zaman gudun hijira a ƙetare, inda ta rera waƙoƙi da dama, a cikinsu har da Soweto Blues.

A ran da aka fara boren, kusan duk kafofin yaɗa labaran duniya ne suka yi ta ba da labarin asarar rayukan da aka yi, musamman buɗe wa matasa, fararen hula wuta, da ’yan sandan gwamnatin mulkin wariya ta Afirka Ta Kudu a wannan lokacin, suka yi. A kan talabijin Jamus, an gabatad da wannan rahton ne kamar haka:-

„A garin Soweto na Afirka Ta Kudu, ana ci gaba da mummunar tarzomar da ta ɓarke. Ya zuwa yammacin yau dai, mutane 35 ne suka rasa rayukansu, 33 daga cikinsu baƙaƙe ne, sa’annan biyu kuma masu farin fata“

Wannan ranar ta 16 ga watan Yuni dai, muhimmiyar rana ce a tarihin ’yan Afirka Ta Kudun. Kamar yadda Peter Magubane, wani shahararren mai ɗaukar hoto na ƙasar, wanda ya ga yadda ababa suka wakana da idanunsa ya bayyanar:-

„Ran 16 da watan Yuni na da matuƙar muhimmanci a tarihin Afirka Ta Kudu. A wannan ranar ne katangar mulkin wariya ta Apartheid ta fara tsagewa. Daga wannan ranar ne dai ƙasa ta fara ɓubbuga a Afirka Ta Kudun. Za a iya kwatanta wannan ranar da farkon ranar da aka fara rusa katangar Berlin a Jamus. Tun wannan lokacin ne ƙasarmu ta sake gaba ɗaya.“

A wannan ranar dai, dubban ’yan makaranta da sauran matasa ne suka shiga zanga-zanga ta hannunka mai sanda, don nuna adawa ga matakin da gwamnatin farar fata ta ɗauka na tilasa musu, su dinga yin amfani da harshen Afrikaans, tamakar harshen koyarwa a makarantun. Harshen Afrikaans ɗin dai, harshen danniya ne. Kai tsaye ne dai aka tura ’yan sanda zuwa gun zanga-zangar, inda kuma ba tare da wata wata ba, suka yi ta buɗe wa ’yan makarantan wuta. Sai kuma ko’ina ya yamutse, al’amura suka yi ta taɓarɓarewa.

Antoinette Sithole, ƙanwa ce ga Hector Peterson, wanda hotonsa ya kewaye duniya. Shi ne dai ɗan yaron nan mai shekaru 13 da ake gani a hotunan wannan tarzomar, wanda wani mutum ya riƙe a hannu, bayan da ’yan sanda suka harbe shi. Ƙanwarsa, Antoinette Sithole, ta bayyana cewa:-

„Da muka doshi makarantar Sakandare ta Orlando, wadda ke kusa da tsohon gidan Nelson Mandela, sai muka ga jami’an tsaro da motocinsu masu sulke, da kuma karnuka. Amma ba mu yi zaton aukuwar wani abin aibu ba, saboda zanga-zangarmu ta hannunka mai sanda ce. To amma, ba zato ba tsammani sai muka dinga jin amon bindiga, sai ko’ina ya yamutse. Ba ma ma iya bambanta harsashin bindiga da kuma barkonon tsohuwa. A cikin wannan hargitsin ne dai aka harbe wâna.“

Hector Peterson dai na ɗaya daga cikin farkon waɗanda suka rasa rayukansu a tarzomar ta Soweto. Gwamnatin Afirka Ta Kudun dai, ta ce mutane 23 ne suka mutu. Amma mazauna Soweton, sun ba da sanarwar cewa yara kimanin ɗari 2 zuwa ɗari 6 ne ’yan sandan suka bindige. Ko’ina dai, a wannan ranar a Soweton, ’yan sanda fiye da dubu da ɗari 5, kuma masu ɗamara kicin kicin da makamai ne suka yi wa duk titunan shiga garin ƙawanya.

Duk da asarar rayukan da aka yi dai, ’yan makarantan na wannan lokacin sun ce, tarzomar ta cancanci a yi ta. Kamar dai yadda wasu daga cikinsu suka bayyanar:-

„Mu ne muka share wa Afirka Ta Kudu fagen samun ’yancinta“

Mafi yawan ’yan Afirka Ta Kudun dai na bayyana ra’ayin cewa, ranar 16 ga watan Yunin, rana ce da ke alamta mafarin wagajewar mulkin wariya ta Apartheid. Ganin yadda ’yan sanda suka yi ta buɗe wa yara ƙanana wuta ne, ya tunzura wasu baƙaƙen shiga yaƙin sunƙuru. ’Yan ƙasar, masu fararen fata da dama ma, ba su amince da wannan matakin ba. A fagen siyasar ƙasa da ƙasa ma, sai Afirka Ta Kudun ta sami kanta cikin wani mawuyacin hali, inda ko’ina, aka fara yi mata saniyar ware. Amma duk da haka, sai da aka ci gaba da gwagwarmayar ƙwato ’yancin baƙaƙen fatan ƙasar, har tsawon shekaru 18, kafin shugabannin mulkin wariya ta Apartheid ɗin su saduda, su miƙa wuya.

A shekarar 1994 ne dai, aka kawo ƙarshen mulkin wariyar a Afirka Ta Kudu, inda kuma a karo na farko a tarihin ƙasar, baƙaƙe da faren fata suka jefa ƙuri’a a farkon zaɓen dimukraɗiyya na ƙasar.

Babu shakka, matasan ƙasar sun taka muhimmiyar rawar gani wajen samo wa al’umman baƙaƙen fata ’yancinsu. Sai dai, akwai bambanci tsakanin matasan shekaru 30 da suka wuce, da na yanzu, inji Anton Meier, wani injiniya a tashar talabijin ta ƙasar, wato SABC. A nasa ganin dai, matasan da ɗin, sun fi na yanzu wayewar kai, a harkokin siyasa.