1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin Bude Cibiyar Nazarin Musulunci A Berlin

December 15, 2004

A yau laraban nan ne aka yi bikin bude wata cibiya ta nazarin al'amuran Musulmi a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/BveC

Cibiyar ta nazarin al’amuran Musulunci, wacce zata rika shirya taruka na kara wa juna ilimi da zaman tattaunawa da rubuce-rubuce bisa manufar wayar da kan Musulmi game da al’amuran siyasa, ba ta da niyyar shiga wata gasa da sauran kungiyoyin Musulmin dake nan kasar ta Jamus. Domin kuwa tun da farkon fari gaggan kungiyoyin Musulmin dake da kakkarfan angizo, kamar kungiyar Milli Görüs da Majalisar Shawara ta Musulmi, suka rika bayyana daridarinsu game da kafa cibiyar. To sai dai kuma kamar yadda aka ji daga bakin darektan cibiyar Abdulhadi Christian Hoffmann, wanda Bajamushe ne da ya rungumi Musulunci, ya nuna cewar wadannan kungiyoyi ba su fito fili suka bayyana adawa da cibiyar ta nazarin al’amuran addinin Musulunci ba. Hoffmann ya kara da cewar:

Ba magana muke yi da yawun illahirin Musulmi a nan kasar ba, saboda ba wanda ya zabe mu domin wakiltarsa. Mu dai taro ne na Musulmi, wadanda suka tsayar da shawarar gabatar da matakan ilimantarwa domin cike gibin ayyukan sauran kungiyoyin Musulmi a nan kasar. Amma mu kan mu ba mu da nasaba da wata kungiya kuma ba mu da niyyar shiga gasa ko tserereniya da sauran kungiyoyi. A takaice ba na zaton muna da wani iko na magana da yawun illahirin Musulmin Jamus.

Ta la’akari da wannan bayani cibiyar ba zata zama wata kafa guda daya da mahukunta ko jami’an coci zasu iya tuntubarta kai tsaye a madadin sauran Musulmi, kamar yadda ministan cikin gida Otto Schily ya dade yana sha’awar ganin ta samu ba. Hoffmann ya ce a duk kasar da ake bin tsarin demokradiyya tilas ne a samu kungiyoyi daban-daban dake da banbancin ra’ayi da manufofi, kuma wajibi ne minista ko mujami‘ar da lamarin ya shafa su hakikance da haka su kuma rika tuntubar kowace daga cikinsu. Ya ce bai kamata a nemi sanya wa Musulmi wata riga ta coci domin zama sharadin musayar yawu da su ba. Babban abin da Hofmann ke fata shi ne ganin Musulmi sun samu ci gaba a nan kasar daidai da yadda lamarin yake a Amurka, inda ake cude-ni-in-cude-ka da su a dukkan harkokin rayuwa ta yau da kullum, kuma ita kanta gwamnati kan nemi shawara daga gare su. Domin cimma wannan buri cibiyar zata yi bakin kokarinta wajen cike gibin da Musulmi ke fama da shi a nan kasar ta yadda za a rika damawa da su a harkoki na siyasa da zamantakewa a maimakon ci gaba da zama saniyar ware. Abin da cibiyar ke bukata a yanzun shi ne wata kafa ta samun kudaden shiga domin ta haka ne kawai kwalliya zata mayar da kudin sabulu dangane da manufofin da ta sa gaba.