1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin baje kolin litattafai a Alkahira

January 18, 2006

An gayyaci Jamus domin zama babbar bakuwa mai martaba a bikin baje kolin litattafai a Alkahira

https://p.dw.com/p/Bu2J
Jamus a bikin baje kolin litattafai a Alkahira
Jamus a bikin baje kolin litattafai a AlkahiraHoto: dpa

An dai saurara daga bakin Jürgen Boos darektan bikin baje kolin litattafai na birnin Frankfurt yana mai nuna cewar gayyatar da aka yi wa Jamus a matsayin bakuwa mai martaba a zauren bikin na birnin Alkahira wani abin alfahari ne ga kasar. Jamus zata yi amfani da wannan dama domin kyautata dangantakar al’adu da kuma musayar ra’ayoyi tsakanin gaggan masana da mawallafa akan muhimman batutuwan dake daukar hankalin jama’a a sassan duniya dabam-dabam a halin yanzun haka. An shirya tarurruka daban-daban na kara wa juna ilimi, inda za a duba batutuwan da suka hada da zamantakewar jama’a da harkar al’adu da ilimi da kuma ire-iren ci gaban da ake samu a harkar binciken al’amuran kasashen larabawa da musulmi a cibiyoyin nazari na kasashen Turai. A matsayinta na babbar bakuwa mai martaba kasar ta Jamus ta tanadar da abubuwa masu tarin yawa da suka shafi al’adun kasar wadanda zata baje su a zauren bikin. Akwai wata kungiya ta kidan al’adun gargajiya da wasu masu wasannin mutum-mutuni wadanda zasu rika kai da komo a zauren birkin mai fadin murabba’in meta dubu hamsin. Kazalika bikin zai samu halarcin mawallafan Jamus tsattsan baki ‚yan kaka-gida domin nuna irin ci gaban da kasar ta samu a zama na cude-ni-in-cude-ka tsakanin kabilu da jinsunan mutane dake zaune a cikinta daga kusan dukkan sassa na duniya. A karkashin taken „Yare daya-al’adu daban-daban“ wasu mawallafan Jamus guda biyu Selim Özdogan da Adel Karasholi zasu halarci zauren bikin baje litattafan na birnin Alkahira domin gabatar da litattafansu. Gidajen litattafan Jamus 163 zasu baje kolin litattafansu a zauren. Jürgen Boos yayi bayani akan haka yana mai cewar:

„Gidajen litattafan na Jamus zasu gabatar da litattafai iri daban-daban kama daga litattafai na yara da matasa zuwa ga litattafan adabi da al’adu da na koyan harshen Jamusanci da fassarar wasu daga cikin litattafan mawallafa na Masar, kazalika da wadanda suka shafi dangantakar al’adu da tuntubar juna tsakanin kasashen Musulmi da na nahiyar Turai.“

Kamar dai yadda muka yi bayani a wannan karon an gayyaci jamus domin zama babbar bakuwa mai martaba a zauren bikin na birnin Alkahira, amma a daya bangaren kuma wakilan kasar ta Jamus na fatan ganin an gayyaci kasar ta Masar domin zama babbar bakuwa mai martaba a zauren bikin baje kolin litattafai na Frankfurt nan da shekaru biyar masu zuwa.