Bikin ƙona makamai a Cote D´ivoire | Labarai | DW | 30.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin ƙona makamai a Cote D´ivoire

Yau ne shugaban ƙasar Cote d´Ivoire Lauran Bagbo zai jagorancin bikin ƙona makamai a birnin Bouake da ya kasace shekaru kussan 5 cikin hannun yan tawayen FN.

Tun ɓarkewar rikicin tawaye a ƙasar Cote d` Ivoire a shekara ta 2002, wannan shine karo na farko, da shugaban ƙasa Lauran Bagbo, ya sa ƙaffa a wannan yanki, a sakamakon yarejeniyar zaman lahia da a ka cimma a birnin Ouagadougou na Bourkina Faso.

Za a wannan gagaramin buki, tare da halaratar shugabanin ƙasashe 7 na Afrika, wanda su ka haɗa da John Kuffor na Ghana, Blaise Kampaore na Burkina Faso, da kuma Tabon Mbeki na Afrika ta kudu.

Shugabankasa da Pramninista Guillaume Sorro za su gabatar da jawwabai a game da zaman lahai da aka samu a ƙasar Cote D´Ivoire.

To saidai a game da wannan batu, har yanzu masu lura da al´ammura na nuna ɗari-ɗari, ta la´akari da ɗigirgiren da yarjeniyar ke yi, wajen tabbatar da zaman lahia mai ɗorewa.