1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ƙona makamai a Cote D´Ivoire

Yahouza S.MadobiJuly 31, 2007

Ra´yoyin jama´a, a game da bikin ƙona makamai a ƙasar Cote D´Ivoire

https://p.dw.com/p/Btur

Jiya ne a birnin Bouake na ƙasar Cote D`Ivoire a ka yi bukin ƙona makamai, a matsayi wani mataki na kawo ƙarshen rikicin tawayen da ya ɗauki tsawan shekaru 5 a ƙasar.

A halin yanzu jama´a, a ciki da wajen Cote D´Ivoire, na ci gaba da tsokaci a game da wannan biki.

Mafi yawan jaridun da su ka hito yau a ƙasar Cote D´Ivoire sun yi tsokaci, a game da wannan biki na ƙona makamai.

Masharahanta da sauran al` ummomin ƙasar sun nunar da cewa babu shakka ziyara farko da shugaba Lauran Bagbo ya kai a birnin Bouake tun bayan shekarau kussan 5 da su ka wuce, ba ƙaramar nasara ba ce ,ta fannin maido da zaman lahia a Cote D´Ivoire da ta yi fama da rikicin tawaye.

To saidai har yanzu akwai sauran rina kaba, wajen cimma birin da aka sa gaba na sake haɗe kan wannan ƙasa.

A yayin da ya ke tsokaci a game da wannan biki, Gilles Yabi na Hukumar da ke kulla da yanayin tashe-tsahen hankulla a dunia, wato ICG ya ce wannan mataki tamkar abun nan ne da Mallam baushe ke cewa „wanda zai sama idan ya hau faifai ya ci gaba“.

A cewar wani jami´in diplomatia dake Cote D´Ivoire, jami´a na sauƙin yaban ɗanyan mai , a game da yunƙurin samar da zaman lahia a Cote D´Ivoire.

Ya zuwa yanzu, a cewar sa, bayan wata 4 da a ka rattaba hannu yarjeniya tsakanin yan tawaye da gwamnati a birnin Ouagadougou, ba a aiwatar da wani abun a zo a gani ba, a daga alƙawuran da aka ɗauka.

Har yanzu ƙasar na rabe gida 2, ga kuma matsaloli kala-kala wanda ba awarware ba.

A cewar wannan jami´i ,halin da ake ciki a ƙasar Cote D´Ivoire, na da mattuƙar ɗaurin kai, ta la´akari da cewar, ga yarjejeniya an cimma, sannan ga shugaban Lauran Bagdo da tsofan abokin gabar sa, Guillaume Soro na gudanar da harakokin mulki kafaɗa da kafaɗa, amma kuma abun mamaki kwanciyar hankali ta kasa tabbata.

A cewar kakakin Praminista Guillaume Soro, samar da zaman lahia mai ɗorewa bayan shekaru da dama na rikici abu ne wanda sai a hankali, amma duk da haka sai hamaddalah idan aka lura da hadin kann da aka samu daga jama´a.