1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bernard Kouchner yayi taron farko a game da Darfur.

Saban ministan harakokin wajen ƙasar France, Bernard Kuchner, ya jagoranci taron farko, a game da yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Kuchner, wanda cemma sannane ne,ta fannin harakokin diplomatia na dunia, ya ce zai iya ƙoƙarin sa domin samun ci gaba, ta fannin kawo ƙarshen rikicin Darfur.

Wannan taro, ya haɗa jami´an diplomatia, da ƙungiyoyin fara hulla, na ƙasar France masu kula da al´ammura a wannan yanki.

A ɗaya wajen, Bernard Kuchner, ya bayyana haɗarin da wannan rikici ya ƙunsa, wajen gurbata zaman lahia a yankin baki ɗaya.