1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Berlin: Karfafa matakan tsaro lokacin gangamin ma'aikata

Zainab Mohammed Abubakar
May 1, 2018

Gwamnatin Tarayyar Jamus ta dauki tsauraran matakan tsaro domin kare rikidewar zanga-zangar ranar ma'aikata ta duniya zuwa tarzoma a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/2wx0S
Myfest am 1. Mai in Kreuzberg
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Hirschberger

A yayin da ake gudanar da bukin ranar ma'aikata ta duniya, gwamnatin Jamus ta girke da jami'an 'yan sanda sama da dubu biyar, domin tabbatar da da cewar, zanga zangar da ake shirin gudanarwa a birnin Berlin, ya gudana lami lafiya.

Duk da cewar tsawon shekaru kenan gangamin kan gudana cikin lumana a Berlin, tun daga ranar daya ga watan Mayu na 1987, 'yan sanda sun sha yin arangama da tarzomar masu ra'ayin rikau a gunduwar Kreuzberg, wanda kan yi muni wani lokaci.

'Yan sanda a Istambul din Turkiyya sun tsare mutane 50 tare da tsaurara matakan tsaro fadin birnin, a yayin da ake gudanar da bukin ranar ma'aikata ta duniya. Bisa al'ada dai, jami'an 'yan sanda kan yi arangama da ma'aikatan da ke zanga zangar neman biya musu bukatunsu a irin wannan rana.

1. Mai-Proteste in Manila, Philippinen
Hoto: DW/A. P. Santos

Jami'an tsaron Turkiyyar sun kawanya wa dandalin taro na Taksim. A hannu guda kuma hukumomi sun tsare dukkan hanyoyin shiga tsakiyar binin na Istanbul.

A birnin Manilan kasar Filipins kuwa wajen mutane dubu biyar suka yi jerin gwano a kan titi tare da kira ga shugaba Rodrigo Duterte da ya cikanta alkawuran da ya daukar wa ma'aikata lokacin yakin neman zabenshi, da rashin aikin yi da ya yi katutu a kasar.

A Indonesiya kuwa ma'aikata akalla dubu 10 ne suka yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa da ke Jakarta, domin gabatar da kokensu musamman karin albashi. Bugu da kari sun bukaci gwamnati da ta kafa dokar haramta baki leburori a kasar, inda acewarsu hakan na kara yawan marasa aikin yi tsakanin 'yan kasar.

Daya ga watan mayu dai rana ce da hutun tunawa da gwagwarmayar ma'aikata Ma'aikata a sassa daban daban na duniya, inda ma'aikatan kan yi amfani da wannan dama wajen yin zanga zangar lumana domin neman a biya musu bukatunsu.