Benoit Hamon ya lashe zaben jam′iyya mai mulkin Faransa | Labarai | DW | 30.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Benoit Hamon ya lashe zaben jam'iyya mai mulkin Faransa

Jam'iyya mai mulkin Faransa ta tsayar da dan takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar nan gaba cikin wannan shekara ta 2017.

A Faransa jam'iyyar Gurguzu mai mulki ta tsayar da dan takara a zaben shugaban kasa, inda Benoit Hamon ya samu nasara a kan tsohon Firamnista Manuel Valls. Shi dai Hamon ya samu kimanin kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben na wannan Lahadi da ta gabata. Kuma tuni tsahon Firaminista Manuel Valls ya rungumi kaddara.

Zaben neman shugaban Faransa za a fafata tsakanin manyan 'yan takara da suka hada da Francois Fillon na jam'iyya mai ra'ayin mazan jiya wanda yanzu haka yake cikin wata badakala, da Marine Le Pen mai matsanancin ra'ayi, gami da Emmanuel Macron matashin da taurariyarsa take haskakawa.

Benoit Hamon tsohon ministan ilimi dan shekaru 49 ya bayyana cewa yana shirye da ya tunkarin kalubanen da duniya ku fuskanta.