Bene: Majalisar dokoki ta yi watsi da gyaran kundin mulki
April 5, 2017Talla
Kudirin shugaban wanda ke neman a kayade wa'adin mulki daya kawai kacal na shekaru shidda ga kowane shugaban da zai hau mulki a kasar, yawancin 'yan majalisun dokokin kasar sun hau kujerar naki a kansa. Sai dai kuma manazarta al'amuran yau da gobe na cewar shugaban kasar na iya shirya kuri'ar jin ra'ayin al'umma a game da wannan batu wanda bisa ga dukkan alamu ya nace sai an yi wadannan sauye-sauye.