Benazir Bhutto ta koma gida Pakistan | Labarai | DW | 18.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Benazir Bhutto ta koma gida Pakistan

Bayan shekaru 8 na gudun hijira tsohuwar FM Pakistan Benazir Bhutto ta koma gida. Dubun dubatan magoya bayanta suka yi mata gagarumar tarba lokacin da ta isa birnin Karachi dake kudancin Pakistan. A girke dubban jami´an tsaro bayan barazanar da ´yan kungiyar al-Qaida suka yi na halaka ta. Bhutto ta ce ta koma gida ne dauke da wani sako na sauyi da kuma fatan inganta makomar mulkin demokiradiya a cikin kasar.