Beljiyam ta dauki matakan dakile hare-hare | Labarai | DW | 26.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Beljiyam ta dauki matakan dakile hare-hare

Mahukuntan Beljiyam na ci gaba da nuna ba sani ba sabo wajen kama wadanda ake zargi da kai hare-hare cikin kasar da kuma na Faransa.

Jami'an tsaro dauke da muggan makamai na ci gaba da karade birnin Brussels na kasar Belgiyam, domin kama wadanda suke da hannu wajen kai hare-hare da birnin ya fuskanta, da kuma birnin Paris na kasar Faransa.

A yammacin wannan Jumma'a da ta gabata an samu fashewar wani abu lokacin da jami'an tsaro suka bankado wani gida da tsageru suka hada bama-bamai, wadanda aka yi amfani da su wajen hallaka mutane 30 yayin da wasu 270 suka samu raunika, lokacin hare-hare a filin jiragen sama gami da tashar jirgin kasa a birnin na Brussels.

A labarin hukumar kula da tashar nukiya ta Beljiyam ta bayyana janye izinin shiga ga wasu ma'aikata, sannan ta hana wasu mutanen damar shiga, bisa tsoron yuwuwar kai hari. Tun bayan hare-haren na ranar Talata mahukuntan sun karfafa matakan tsaro a tashar nukiyar ta Beljiyam.