1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljium: Shekara guda da kai harin ta'addanci

Zainab Mohammed Abubakar
March 22, 2017

A daidai wannan rana ce a shekarar da ta gabata aka kai wasu munanan harin bama-bamai a tashar jirgin kasa da ke filin sauka da tashin jiragen sama na Brussels, harin da ya kashe mutane 32.

https://p.dw.com/p/2ZjTs
Brüssel Gedenken  Schuman-Platz im Europa-Viertel Denkmal
Hoto: DW/B. Riegert

Sarki Philippe na Beljium ya yi kira ga al'ummar kasarsa da su zauna lafiya da juna, kana su rika la'akari da gazawarsu, a wani mataki na daukar darasi da kaucewa sake fadawar kasar cikin wani wadi na tasaka mai wuya, na muggan harin bama-bamai har sau uku da ya kashe mutane 32 a Brussels a bara.

Ya yi wannan furucin ne a daidai lokacin da ake juyayi na cika shekara guda da aukuwar harin da kazalika ya raunata mutane 300. Inda sarkin ya kai ziyara ga mutanen abun ya ritsa dasu.

Sarki Philippe ya ce "da yawan mutane marasa adadi da suka tsinci kansu cikin yanayi makamancin wannan, muna tayaku bakin ciki. Bari na sake jaddada cewar, hakki ya rataya a wuyan kowanne daga cikinmu, na tsabtace al'ummarmu. Mu ko yi darajawa juna, tare da sanin alakar da muke da shi da kowa. Ta hakan ne zamu cimma nasarar kare kanmu".

Tun da farko Sarki da Sarauniya Mathilde sun hade da Fraiminista Charles Michel da sauran ministocin gwamnati, wajen kai ziyara inda harin ta'addancin ya auku a filin jiragen sama da ke Brussels.