BBOG ta bai wa Najeriya wa'adi
March 13, 2018Talla
Kungiyar nan da ke fafutikar ceto 'yan matan makarantar Chibok a Najeriya ta zargi gwamnatin kasar da abin da ta kira rashin kwarewa da kuma sakaci dangane da 'yan mata 110 da aka sake sacewa a shiyar arewa maso gabashin kasar.
Kungiyar ta Bring Back Our Girls, ta yi kaurin suna ne a fafutikar neman kubutar da 'yan matan Chibok 276 da kungiyar ta Boko Haram ta kwashe su kimanin shekaru hudu da suka gabata.
Ta dai bai wa gwamnatin Najeriya kwanaki bakwai na tabbatar da ceto 'yan matan Dapchi 110 da aka kwashe a watan jiya da ma na Chibok 112 da suka saura a hannun kungiyar Boko Haram.