1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayern Munich ta kori Carlo Ancelotti

Ahmed Salisu
September 28, 2017

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kori mai horas da 'yan wasan kungiyar Carlo Ancelotti, bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun kulab din PSG a gasar cin zakarun Turai.

https://p.dw.com/p/2ku01
Bayern Münchens Trainer Carlo Ancelotti
Hoto: Picture-Alliance/dpa/Ballesteros

A wani sako da ta sanya a shafinta na intanet kungiyar ta Bayern Munich ta ce ta yanke wannan shawara ce ta raba gari da Ancelotti bayan wani dogon nazari da ta yi. Tuni dai kungiyar ta sanar da mika ragamar horas da 'yan wasan Munich din ga Willy Sagnol wanda zai kasance koci na wucin gadi kafin daga bisani ta fidda wanda zai jagoranci kungiyar.