Bayan zaɓe a Iraƙi | Labarai | DW | 08.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bayan zaɓe a Iraƙi

Martanin da jami'an Iraki game da zaben majalisar wakilai.

default

Ɗan ƙasar Iraƙi na nuna yatsarsa da tawwadar zaɓe.

Shugaban Amirka, Barack Obama, ya nuna jin daɗinsu game da yadda zaɓen Iraƙi ya gudana a jiya. A cikin jawabin da ya yi a birnin Washington, Obama ya yaba da yadda al'umar ƙasar suka fito ƙwansu da kwarkwatansu don kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na majalsar wakilai da ke zaman irinsa na biyu tun bayan mamayar da Amirka ta yi wa ƙasar a shekara ta 2003. Shugaban na Amirka ya ce za a fuskanci mawuyacin hali nan gaba. Ya kuma nanata alƙawarinsa na janye rundunar Amirka daga ƙasar ta Iraƙi nan da watan Agusta. Sama da rabin al'umar ƙasar ne dai suka kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na jiya duk da aukuwar hare-haren bama-bamai da suka yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 38. Nan da wasu 'yan kwanaki ne dai ake sa ran samun sakamakon zaɓen a baya ga abin da manazarta suka kira doguwar muhawara da za a tafka domin kafa gwamnatin gamin gambiza. Ƙiyasin da aka samu tun da farko daga jam'iyyun siyasar Iraƙi ya yi hasashen samun nasarar gwamnatin gamin gambizar da Framinista Nouri Al-Maliki ke wa jagora. Hukumar zaɓen ƙasar ta ba da sanarwar da ke nuni da cewa mai yiwuwa ne a samu sakamakon zaɓen nan da ranar Alhamis. Amma Abbas al-Bayati daga gwamnatin gamin gambizar al-Maliki ya ce labaran da suka zo musu daga wakilansu sun yi nuni da samun nasarar 'yan takararsu a birnin Bagadaza da kuma kudancin ƙasar da ke zaman maƙarfafa ga 'yan Shi'a.

Mawallafiya: Halimatu Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala