Bayan zaɓe a Afirka Ta Kudu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 04.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Bayan zaɓe a Afirka Ta Kudu

Jaridun sun fi mayar da hankali kan Afirka Ta Kudu bayan zaɓe sai rikicin Darfur da kuma halin da ake ciki a janhuriyar Demokuraɗiyya Kongo.

default

Taya Jacob Zuma murnar lashe zaɓe a Afirka Ta Kudu

A wannan makon ma dai kamar yadda aka saba jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran nahiyar Afurka, inda misali jaridar Süddeutsche Zeitung ta sake leƙawa Afirka ta Kudu domin duba irin alƙawururrukan da Jacob Zuma yayi wa talakawan ƙasar in har ya ɗare kan karagar shugabanci da kuma irin ƙwarin guiwar dake tattare da masu zuba jari na ƙetare. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Makomar manufofin tattalin arzikin Afirka ta Kudu ta danganci fasalin da za a bai wa majalisar ministoci ne da za a naɗa bayan rantsar da sabon shugaba a ranar tara ga watan mayu. Shi dai yanzu ministan kuɗi na Trevor Manuel ya taimaka wajen janyo hankalin 'yan kasuwa na ƙetare zuwa ƙasar ta Afirka ta Kudu. A lokacin da ya kakkaɓe hannunsa daga wannan muƙami sakamakon rikici tsakanin tsofon shugaba Mbeki da shugaba mai jiran gado Jacob Zuma shekarar da ta wuce, a cikin ƙiftawa da bisimilla farashin hannayen jari yayi ƙasa da Johannesuburg. Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar Zuma na sha'awar barinsa akan wannan muƙami. To sai dai ba wanda ya san irin tasirin da rikicin kuɗi zai yi akan Afirka ta Kudu, wanda hakan zai shafi makomar jin daɗin rayuwar talakawan ƙasar."

Sudan, Kinder in einem Flüchtlingslager in Darfur

Yara a wani sansanin ´yan gudun hijira a Darfur

'Yan gudun hijira a lardin Darfur na ƙasar Sudan suna ci gaba da fama da mawuyacin hali na rayuwa sakamakon ƙarancin abinci da ruwan sha. Wannan shi ne bayanin da jaridar Der Tagesspiegel tayi a cikin rahotonta dangane da Sudan. Jaridar ta ce:

"Tun dai bayan da kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifukan yaƙi ta fito da umarnin cafke shugaba Al-Bashir na Sudan, an fatattaki ƙungiyoyin taimako 13 daga ƙasar, lamarin da ya jefa 'yan gudun hijira kimanin miliyan biyu da dubu ɗari bakwai cikin mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi. Domin kuwa ragowar ƙungiyoyin taimakon da suka yi shaura a Sudan ba zasu iya cike giɓin da ya samu ba."

A can janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo ma farar fula na cikin hali na ruɗu da rashin sanin tabbas sakamakon bata kashin da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun sa kai na 'yan Hutun Ruwanda dake kai hare-hare a gabacin ƙasar. A lokacin da take gabatar da rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

Kongo Flüchtlinge an Grenze zu Uganda

Matsalar ´yan gudun hijira a Kongo

"Farar fula a yankin gabacin Kongo suna cikin wani hali na tsaka mai wuya tsakanin sojojin haɗin guiwa na ƙasashen Kongo da Ruwanda a ɓangare guda da kuma dakarun 'yan tawaye na Hutu a ɗaya ɓangaren. A tsakiyar wannan makon sojan gwamnati suka gabatar da mataki na biyu na kutse a lardin arewacin Kivu inda ƙungiyar tawaye ta FDLR ke tsaurara hare-harensu. Su kuma sojojin gwamnati na fatattakar mutane daga gidajensu. Dukkan ɓangarorin biyu dai ana zarginsu da miyagun laifuka na yaƙi."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal