BAYAN KISAN KIYASHIN BURUNDI SAI A CE KAICO AFIRKA ! | Siyasa | DW | 18.08.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

BAYAN KISAN KIYASHIN BURUNDI SAI A CE KAICO AFIRKA !

Rikici a yankin manyan tafkunan na na gabashin Afirka dai ya ki ci ya ki cinyewa. Kisan kiyashin baya-bayan nan da aka yi a kasar Burundi, ya dusashe duk wata fatar da ake yi na samad da zaman lafiya mai dorewa a kasashen yankin, kamarsu Uganda, da Ruwanda da kuma gabashin Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango.

`Yan gudun hijiran kasar Burundi, a kan wani itace, yayin da suka iya tsallakewa zuwa Tanzaniya.

`Yan gudun hijiran kasar Burundi, a kan wani itace, yayin da suka iya tsallakewa zuwa Tanzaniya.

Masharhanta dai na ganin cewa, rikicin da aka shafe shekaru aru-aru ana ta yi a yankunan manyan tafkin nan na gabashin Afirka na da asali ne daga dalilan siyasa, inda ake amfani da kabilanci wajen ta da zaune tsaye.

Hakan ne dai ya janyo mummunan kisan kare dangin nan da ya auku a kasar Rwanda. A halin yanzu kuma, wannan salon ya yadu zuwa kasar Burundi, yana kuma barazanar janyo wata mummunar annoba ga kananan kabilun da tun da ma can, ke ta hamayya da juna a gabashin Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango.

Tun kafin samun `yancinsu ne dai kasashen Rwanda da Burundi ke ta huskantar barazanar yakin kabilanci. Shekaru 30 bayan samun `yancin kuma, kurar rikici dai ba ta lafa ba. Saboda har ila yau, `yan kabilun Tutsi da Hutu na nan na ta arangama da juna wajen yada angizonsu da kuma mamaye madafan iko, kamarsu rundunar soji, da hukumomi, da harkokin cinikayya da na ilimi, a kasashen biyu. A halin yanzu dai, `yan Tutsin ne ke rike da madafan iko a Burundi, sa’annan `yan Hutun kuma ke jan ragamar mulki a Rwanda. Babu dai alamun samun sassaucin tsamari da ya hauhawa a yankin. Al’amura ma sai kara tabarbarewa suke yi.

Wannan rikicin dai, a hankali yana yaduwa zuwa gabashin Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango, inda `yan siyasar kabilun biyu ke amfani da bambancin kabilancin da ake samu wajen cim ma burinsu – wato na mamaye da kuma dawwama kan madafan iko. Ta hakan ne dai, `yan kabilar Hutu ke ci gaba da fatattakar, wadanda aka yi wa lakabin Banyamulenge – a kasar Kwango. Su dai `yan Banyamulengen, wato asalinsu, `yan kabilar Tutsi ne da suka yi kaura zuwa Kwangon daga Rwanda. To yanzu kuwa, su ake gani ko kuma dauka kamar `yan tawaye.

Babu dai wani uzuri da zai hujjanta wannan danyen aikin, na yi wa wasu tsiraru kisan kiyashi. Gwagwarmayar da ake yi na mamaye madafan iko ne kawai ke sa masu jan ragamar mulki a yankin, rashin auna sakamakon da matakan da suka dauka za su janyo. Ta hakan ne kuwa ake ta ci gaba da huskantar annoba iri-iri a wannan yankin, inda a halin yanzu, saboda rudamin da ake ciki, ba a ma iya bambanta, masu kai hari da wadanda ake cin zarafinsu, da masu laifi da wadanda aka kwara.

Har ila yau dai gamayyar kasa da kasa da kasa ta kasa shawo kan wannan bala’i na nuna kiyayya da kyama ga juna a yankin. kasashen da rikicin ya shafa kuma, sun gaza cim ma wata madafa, saboda son zuci da `yan tsagerun yankin ke bi. Duk wani matakin da za su yunkuri dauka, sai ya ci tura.

Ba za a iya dai yi zancen zaman lafiya a kasar Rwanda ba, muddin rabibn kabilun kasar, na zaune a ketare cikin wani mawuyacin hali. Kazalika ma a Burundin, samun zaman lafiya zai kasance abu ne mai wuya, saboda har ila yau, wasu tsiraru ne kawai ke rike da manyan mukaman rundunar sojin kasar. Sabili da haka, ko wace yarjejeniya aka cim ma ma, sai ka ga a lokaci daya, sun sa kafa sun shure ta.

 • Kwanan wata 18.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhD
 • Kwanan wata 18.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhD