Bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 19.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Bayan juyin mulkin da wasu sojoji suka yi yanzu haka ƙura ta lafa.

default

Sojoji sun tumɓuke Tanja Mamadou

A ƙasar Nijar bayan juyin mulkin da wasu sojoji suka yi yanzu haka harkoki sun koma tafiya kamar yadda aka saba. Kasuwanni da bankuna da makarantu duk sun kasance a buɗe. Wasu sojoji ne ƙarƙashin jagorancin Manjo Adamu Haruna suka kifar da gwamnatin Tanja. Sojojin sun naɗa skwadron Salou Djibo a masayin jagoran na sabon gwamnatin CSRD ta sake dawo da mulkin dimokradiyya. Ƙungiyar AU ta kasashen nahiyar Afirka ta yi tur da Allah wadai da juyin mulkin yayin da ita ma ƙasar Jamus a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana rashin jin daɗinta a kan juyin mulkin tare da fatan gani sojojin da suka kwaci mulki sun maido da tsarin mulkin dimokradiyya cikin gaggawa. A ƙasa kuna iya sauraron sauti. Akwai ƙarin bayani daga wakilinmu dake Yamai, da kuma hira da masanin harkar siyasa a Najeriya. Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Thomas Mösch

Sauti da bidiyo akan labarin