Batutuwan da suka kada Afirka a 2016
Hare-haren ta'addanci da bore. Shugabannin kama karya, da ke son makalewa kan mulki, da wadanda suka amince da shan kaye a zabe, da suka taya wadanda suka ci murna. Waiwayen batutuwan Afirka a 2016.
Ta'adda a wurin shakatawa na gabar Teku
A watan Maris masu kishin addini sun kashe akalla mutane 19 a wurin shakatawa na Grand Bassam da ke Cote d'Ivoire. Ba shi ne harin farko irinsa ba: A watan Janeru 'yan Al-Qaida reshen Magrib sun farma wani otel a Ouagadougou a Burkina Faso, sun kashe mutane da yawa. Hakan ya faru makonni kadan bayan rasa rauka a wata garkuwa da aka yi da mutane a birnin Bamako. Ta'adda ta mamaye Afirka ta Yamma.
Daurin rai da rai ga tsohon dan mulkin kama karya na Chadi
An yanke wa Hissène Habré hukuncin daurin rai da rai saboda aikata laifin yaki. An yi kiyasi mutane dubu 40 aka kashe a Chadi lokacin mulkinsa na tsawon shekaru takwas daga 1982. Wata kotu ta musamman ta 'yan Afirka zalla a Senegal ta yanke masa hukuncin. Kungiyar Tarayyar Afirka ta kafa kotun, domin Senegal ta ki amincewa ta tasa keyar Habré ga kotun kasa da kasa da ke birnin The Hague.
Adalci ga kayayyakin al'adun gargajiya a Mali
A ranar 19 ga watan Satumba an sake bude masallacin Sidi-Yahya da ke Timbuktu. Cikin sa'o'i a 2012 masu kishin addini suka ruguza masallacin. An dauki watanni biyar kafin a kamalla gyaran kofarsa. Kotun kasa da kasa ta birnin The Hague ta yanke wa Ahmad Al Mahdi hukuncin daurin shekaru tara a kurkuku bisa laifin lalata masallacin da ke a jerin kayayyakin tarihi na duniya. Hukunci ne na tarihi.
Kotun duniya da aka tsana
Duk da wannan hukunci da ya sha yabo, sukan lamirin kotun ta kasa da kasa na kara yin yawa, musamman a Afirka: Kotun ta sanya wa kasashen Afirka karan tsana yayin da take sako-sako da bin ba'asin wasu laifuka da ake aikatawa a wasu sassan duniya. Burundi da Gambiya da Afirka ta Kudu sun janye daga kotun. Watakila don kare shugabanninsu? Zargin da masu sukan lamirinsu ke yi ke nan.
Dunkule hannu don fafatukar kyautata rayuwa
A wasan gundun dogon zango na Olympics a birnin Rio, Feyisa Lilesa ya kammala gudun hannunsa a dunkule kan kanshi. Alama ce ta nuna adawa da gwamnatin Habasha da yadda take muzguna wa kabilarsa ta Oromo. A kasarsu yin wannan alama babban hadari ne: A watan Oktoba a Bishoftu sojoji sun yi harbi cikin jama'a da suka yi wannan alama, an yi turmutsitsi, inda mutane kusa 50 suka mutu.
Fata ga 'yan matan Chibok a Najeriya
Bayan shekaru biyu da rabi, a watan Oktoba iyayen 'yan mata 'yan makaranta 21 da aka yi garkuwa da su, sun sake ganin 'ya'yan nasu. Hakan nasara ce ta tattaunawa tsakanin Najeriya 'yan Boko Haram. Amma har yanzu akwai 'yan mata da yawansu ya ninka wannan har sau 10 a hannun Boko Haram, da har yanzu take addabar yankin Arewa maso Gabacin Najeriya da yankunan kan iyakarta da kasashe makota.
#ThisFlag: Malamin coci na matsa kaimi
Malamin coci a Zimbabuwe, Evans Mawarire ya hada kan mutane a yekuwarsa mai taken: "Launin kore a tutocinmu na ma'anar albarkatun noma da muka girba. Amma ba ma ganin komai a ciki!", inji shi a wani faifayen bidiyo da aka watsa ta shafukan sada zumunta. A watan Yuni dubbannin mutane ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da matsin hali na rayuwa karkashin jagorancin Shugaba Mugabe.
Bore a Kwango
'Yan adawa da kungiyoyin farar hula sun fantsama kan tituna a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, suna nuna bukatar a sake gudanar da zaben shugaban kasa a 2016 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Amma Shugaba Kabila ya ci gaba da rike madafun iko. A watan Disamba wa'adin mulkinsa na biyu ya kare, ba zai iya yin takara ba. Sai dai ya bari an dage gudanar da zabe. Watakila har zuwa 2018.
Shugaban Afirka ta Kudu a cikin kaka-ni-kayi
Jacob Zuma ya fuskanci babbar turjiya a 2016. Rahoton mai kula da batun cin hanci Thuli Madonsela ya nuna kamfanin iyalan Gupta na da angizo babba a harkokin siyasar kasar. Amfani da kudin kasa wajen kwaskware gidansa ya zame masa alakakai. 'Yan kasa da takwarorinsa na jam'iyya sun yi kira da ya yi murabus. Amma Zuma ya yi kunnin kashi - ya tsallake kuri'ar kin amincewa da shi a majalisar dokoki.
Karancin kudi da juyayi a Mozambik
Fashewar wata motar dakon man fetur a lardin Tete a Mozambik ta kashe mutane fiye da 70. Hatsarin ya auku lokacin da mutane ko kakarin tatsar mai daga motar. Wannan abu ne da ke iya faruwa a wata kasa da ta talauce bayan babbar badakalar cin hanci da rashawa. Bugu da kari ana samun yake-yake tsakanin sojoji da 'yan tawaye bangaren 'yan adawa, ga kuma rikicin gwamnati da aka kasa warwarewa.
Abin al'ajabi a Gambiya
Ba zato ba tsammani aka zabi Adama Barrow a mukamin sabon shugaban kasar Gambiya, da zai gaji Yahya Jammeh, wanda ke mulkin kama karya tun shekaru 22. Wani sabon abin mamaki shi ne: Jammeh ya amince da shan kaye, amma kash bayan wasu makonni ya lashe amansa, inda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara. Daukacin 'yan Gambiya dai na ci gaba da fatan cewa lalle abin al'ajabin zai tabbata.
Ghana ta nuna yadda ake yi
A fagen demokradiyya, Ghana na ci gaba da zama abin koyi. Dan takarar 'yan adawa Nana Akufo-Addo ya lashe zaben shugaban kasa na watan Disamba. Sau biyu yana takara yana kuma shan kayi. Shugaba mai ci John Mahama ya taya shi murna ya kuma amince da shan kaye. Masu zabe sun yanke hukunci, domin Ghana na fama da koma bayan tattalin arziki da matalsar makamashi da yawan marasa aikin yi.
Bankwana da Papa Wemba
An sha yayata jita-jitar mutuwar Papa Wemba. Amma lokacin da ajalinsa ya yi mawakin mai shekaru 66 dan kasar Kwango bai bada damar nuna shakka ba. A kan dandamalin bikin kidi a birnin Abidjan na Cote d'Ivoire ya yanki jiki ya fadi. Duniya ta yi rashin dan salon kidan Rumba da ya fitar da sunan Kwango a duniya a fagen waka. Ya ce ba kade-kaden Kwango ko na Afirka yake yi ba, shi kidansa yake yi.