1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun tsige shugaban kasar Malawi ya samu koma baya

January 9, 2006
https://p.dw.com/p/BvD0

Daya daga cikin yan majalisar dokokin kasar Malawi ya janye kudurin daya gabatar a gaban majalisar na tsige shugaban kasar, wato Bingu Mutharika daga mukamin sa.

A cewar dan majalisar mai sunas, Maxwell Milanzi, ya dauki wannan matakin ne bayan daya gaza samun cikakken goyon bayan yan kasar game da wannan kuduri nasa.

A can baya dai dan majalisar ya bukaci a tsige shugaban ne, bisa laifuffuka dake da nasaba da cin hanci da kuma rashawa a hannu daya kuma da almubazzaranci da dukiyar kasa.

Tun dai lokacin da aka fara rade raden tsige shugaban, kasashen dake bawa kasar tallafin raya kasa irin su Biritaniya suka yi gargadin cewa aiwatar da wannan mataki ka iya jefa kasar cikin wani sabon rudani na siyasa.

A yanzu haka dai an kiyasta cewa akwai yan kasar ta Malawi kusan miliyan biyar dake fama da karancin abinci a fadin kasar baki daya.

Daukar wannan matakin dai ya biyo bayan kokarin da yan majalisar kasar keyi ne na ganin an samu zaman lafiya da kuma natsuwa a al´amurran siyasa a fadin kasar baki daya.