1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Talauci da zabe a Afirka sun dauki hankalin jaridu a Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
September 21, 2018

Ta tabbata cewa Najeriya ta kasance kasar da ta fi kowacce yawan matalauta yanzu a duniya duk da irin nasararorin da ake cewa nahiyar Afirka na samu a fannoni na ci gaba.

https://p.dw.com/p/35IR6
Thema - Binnenflüchtline in Nigeria
Hoto: DW/Uwaisu Idris

Za mu fara ne da labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta dangane da sabon rahoton bankin duniya dangane da matsayin talauci a duniya.

Labarin mai taken "mafi yawan wadanda ke cikin kangin talauci na yankin Afirka kudu da Sahara" na cewa a yanzu haka Najeriya ta maye gurbin kasar Indiya a matsayin kasar da ta fi kowacce yawan matalauta a duniya, bisa ga hasashen bankin duniya. Wannan dai ba labari mai dadin ji ba ne bisa la'akari da nasarori da Afrikar ta samu a shekarun baya, wanda kuma ke nuni da cewar fatan cimma nasarar yakar talauci nan da shekara ta 2030 tamkar ya koma mafarki.

Sai dai a bangaren Majalisar Dinkin Duniya har yanzu wannan nasara ce, ganin cewa cikin shekaru 25, sama da mutane biliyan daya sun kauce wa rayuwar kunci cikin talauci, saboda suna iya samun kusan dala biyu a kowace rana bisa ga kiyasin shekarar 2011. A shekara ta 2015 bankin duniya ya samu mutane kimanin miliyan 736 wadanda ke rayuwa cikin matsanancin talauci. Sama da kashi 50 daga cikin 100 na yawan mutanen da ke cikin kangin talauci na zaune ne a kasashen Afirka da ke yankin kudu da Sahara, yayin da daga cikin kasashe 27 mafi talauci a duniya, 26 na nahiyar Afirka.

 

Daga batun talauci a nahiyarmu ta Afirka sai kuma shirye-shiryen zabuka masu gabatowa. A sharhin da ta rubuta mai taken "Takaddama kan sabon tsarin zabe" jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce hukumar zabe ta tantance sunayen 'yan takarar kujerar shugaban kasa, sai dai 'yan adawa sun yi gargadin a guji yin magudi.

Kongo Emmanuel Ramazani Shadary
Hoto: REUTERS

Jaridar ta ci gaba da cewar, tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 1960, ba'a taba yin zabe a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ba. Amma hakan na shirin sauyawa a watan Disamba, idan aka zabi wanda zai karbi mulki daga hannun Shugaba Joseph Kabila. A wannan Larabar ce dai hukumar zaben ta tabbatar da sunayen 'yan takara 21 da za su fafata a zaben na ranar 23 ga watan Disamba.

Daga cikin manyan 'yan siyasar da za su fafata a zaben shugaban kasar da ke tafe akwai Ramazany Shadary dan takarar bangaren masu mulki, a yayin da bangaren adawa ke da irin su Felix Tshisekedi na jam'iyyar UDPS da Vital Kamerhe na jam'iyyar UNC. Shadary da ke zama tsohon ministan harkokin cikin gida na zama na hannu daman Shugaba Kabila, wanda ke nuni da cewar idan har ya samu nasara, tamkar Kabila ne zai ci gaba da jan akalar kasar ta Kwango daga bayan fake.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

A Najeriya kuwa batun sayen takardun takarar fidda gwani a jam'iyyar adawa ta PDP shi ne ya dauki hankali a wannan makon. Jaridar die Tageszeitung  ta ce daruruwan mutane ke yin cincirindo a harabar hedikwatar babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ke birnin tarayya, Abuja. A yanzu haka dai ana ta sayen takardun takara, gabanin zabukan fidda gwani da ke tafe a ranakun biyar zuwa shida ga watan Oktoba da ke shirin kamawa, duk da cewar sai cikin watan Fabrairun shekara ta 2019 ne, Najeriyar za ta gudanar da zaben shugaban kasa.