Batun mayarda Charles Taylor gida | Labarai | DW | 13.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Batun mayarda Charles Taylor gida

Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya tattauna da takwaarnsa na Afrika ta Kudu Thabo Mbeki game da batun mayarda tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor gida.

Kakakin gwamnati Remi Oyo ta baiyana haka kodayake bata kara wani bayani game da ziyarar da Mbeki ya kaiwa Obasanjo ba a daren jiya,amma majiyoyi daga Liberia sun fadi tun farko cewa Obasanjo zai tattauna da shugabanin Afrika kafin mika Taylor ga kasarsa.

A watan agusta na 2003 ne dai Obasanjo da Mbeki suka shawo kan Charles Taylor ya sauka daga mulki ya kuma amince da zaman mafaka a Najeriya,a kokarinsu na kawo karshen yakin basasa ba shekaru 14 a kasar ta Liberia.