1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun gwajin ƙwayar halitta kafin samun visa

December 14, 2007

An fara kokawa game da batun gwajin ƙwayr halittar anan Jamus

https://p.dw.com/p/CbWd
Hoto: DW

Aung Parveen ɗan kasar Burma ne da aka karɓe shi zaman gudun hijira anan Jamus fiye da shekaru 4 yanzu.Inda yayi tunanin cewa yanzu lokaci yayi da iyalinsa zasu su zo su zauna da shi.Amma a lokacinda ya bukaci takardun visa ga iyalin nasa daga hukumomin Jamus ,tsauraran hanyoyi da aka ce ya bi sun matuƙar ba shi mamaki.Lauyansa Andreas Cochlovius ya ce

“hukumomin na Jamus ba su amince da takardar shaidar haihuwarsa ba,saboda haka ofishin jakadancin Jamus a Burma ya nemi yin gwajin ƙwayar halittar jikinsa don tabbatar da cewa shi ya haifi ɗan da yake son azo da shi”

Cochlovius yace babu wata hujja ta sharia da tace a yi wannan gwaji.A raayinsa dokokin Jamus sun amince ne da gwajin ƙwayar halittar jikin mutum a batuwa kamar aikata muggan laifuka,da suka haɗa fyaɗe ko kisan kai.Abinda ofisoshin jakandancin Jamus suke yi na neman gwajin ƙwayar halittar jikin mutum don neman takardar iznin shiga ƙasar baya bisa doka.

“kuma gwajin yana da tsada wanda ba zai yi yiwu wannan mutumi ya iya biya ba.Ana bukatar kimanin dala dubu ɗaya da ɗari shida,kuma dole ne ya biya kafin ayi wanna gwaji”

Duk da haka da alamun hukumomin Jamus suna ci gaba da neman yin gwajin.A lokuta da dama a ƙasar ta Burma dama Afrika ofisoshin jakadancin Jamus su kan nuna shakku game da takardun da mutum yake miƙawa don neman zuwa ƙasar.Maaikatar harkokin wajen Jamus ta ce tana ƙoƙarin tantance masu mika takardun ƙarya ne ko na Jebu.Peter Schneider daga cibiyar harhaɗa magunguna a Cologne yace ya gudanar daruruwan irin waɗannan gwaje gwaje ga masu neman takardun visa ga iyalinsu kuma akwai takardu da yawa a gabansa na neman wannan gwaji:

“a ganina wasu na wannan gwaji ne bisa raɗin kai,wasu daga cikin masu neman takardun da suke zuwa mana mun san cewa suna ganin idan ba tare da gwajin ba iyalinsu ba zasu samu takardun ba”

Saboda haka ne masu sassaucin raayi a majalisar dokokin Jamus suka bukaci gwamnati ta sake yin ƙarin haske kan wannan doka ta gwajin ƙwayar halittar mutum.Hartfrid Wolff member ne na jamiyar,kuma yace:

“anan jamus mutum yana da ‘yancin kin kin bada bayanai kan ƙwayar halittar jikinsa ,saboda haka ne bamu amince mutum ya miƙa wadannan bayanai a hukumomin dake bakin iyakokin kasa ba”

Peter Schneider yace bai yarda cewa masu neman takardun visa ga iyalansu suna ƙokarin yiwa hukumomin wayo ne ba:

“mutane kalilan ne muka samu,musamman uba da ba shi ya haifi dan ba,wanda su kansu sunyi mamakin cewa ba sune suka haifi yaran ba kuma sun matukar nuna ɓacin ransu”

Aung Parveen ɗan kasar ta Burma ya yi imanin cewa shi ya haifi yaron da yake son a taho da shi,saboda haka a ganinsa zasu yi bukin kirsimeti tare da shi anan Jamus.

Lauyansa Andreas ya rigaya ya ɗauki matakai na sharia kan hukumomin Jamus haka kuma wata kotu a Berlin ta yanke hukunci cewa ba dole ne Parveen ya amince da gwajin ƙwayar halittar jinkinsa ba kafin samun takardun Visa ga Iyalansa.sai dai kuma lauyan yace akwai mutane da dama da suke fuskantar wannan matsala.