1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

BATUN DALIBAN KETARE DA KARATU MAI ZURFI A NAN JAMUS

Da can dai, daliban kasashen ketare ba su damu soasai da zuwa nan Jamus kara iliminsu ba, musamman ma dai wadanda ke son yin digirinsu na koli. Game da hakan ne kuwa, jami'an kula da harkokin ilimi na tarayya gaba daya suka yi gangami, inda suka bayyana cewa, a lokaci mai tsawo, wannan halin zai iya janyo wa tattalin arzikin Jamus wani babban cikas. Don shawo kan wannan matsalar ne kuwa, kungiyar musayar daliban nan DAAD, ta yi ta gabatad da tallace-tallace a kafofin sadaswan kasashen ketare, da nufin bayyana wa daliban wadannan kasashen, fa'idar zuwa Jamus don zurfafa iliminsu. Hakan kuwa ya janyo hankullan dalibai da yawa, wadanda da can ba su tuntubi ma zuwa nan Jamus ba.

A shekara ta 2001, kusan daliban kasashen ketare dubu 3 ne suka mika takardunsu na neman zuwa Jamus yin karatun digiri na biyu ko kuma Masters a turance. A shekarar bara kuma, yawansu ya kai dubu 5. A zaihri dai, wannan wani abin fara'a ne ga jami'o'in, wadanda kafin hakan suke ta koken-koken samun karancin dalibai daga ketare. Amma, sai kuma aka wayi gari, yawan daliban da ke neman shiga jami'o'in daga ketare ya habaka, har ma aka gaza amsa duk takardunsu a cikin lokaci. Sabili da hakan ne kuwa, wasu jami'o'in suka gatad da wani sabon tsari na jarraba daliban ta hanyar Internet, kafin ma su sami takardun amincewa da zuwansu nan Jamus. Farfesa Manfred Glesner, na jami'ar kimiyya da fasaha ta Darmstadt, wanda kuma shi ne ke kula da musayar dalibai a fannin Injiniya na na'urorin sadaswa da yada labarai a wannan jami'ar, ya bayyana cewa, wannan jarrabawar da ake fara yi wa daliban na da muhimmanci kwarai:-

"A bangare daya dai, muna farin ciki da yadda kafar DAAD ta tallata harkokin ilimin Jamus a kasashen ketare, inda ta janyo hankullan dailbai da yawa zuwa nan kasar. Amma kafin wani ya taso daga kasarsa zuwa nan Darmstadt, kamata ya yi musan ko wane ne shi, mu kuma iya sanin ko zai dace da fannin karatun da ya zaba. Wannan tsarin dai na da fa'ida. Su jami'o'in suna da tabbacin cewa, sun zabi daliban da suka fi cancanta, su kuma daliban za su ga cewa lalle ne gun da za su je yin karatun shi ya fi dace musu."

Ta hanyar Internet din dai, ana iya shirya kome, tun lokacin da daliban ma ke kasashensu. Ta wannan hanyar ne ma ake iya jarraba daliban a ga cewa, ko shin za su iya karatu a wannan fannin da suka zaba. Farfesa Glesner dai, yana yabon wannan tsarin na jarraba daliban ta hanyar Internet. A lal misali a shekarar bara, kusan dalibai dubu da dari 6 ne suka nemi izinin fara karatu a fanninsa. Amma fannin kuma, dalibai 60 kawai zai iya dauka. Ta fara jarraba daliban dai, an sami sauki wajen zaban wadanda suka fi cancantar shiga jami'ar. Sai dai, ko wace jami'a na da tata jarrabawar daban. A ganin janar-sakatare na kungiyar DAAD dai, kamata ya yi a canza wannan salon, a tsara jarrabawa ta gama gari, wanda duk daliban za su dauka a lokaci daya:- "Ina ganin cewa, can gaba dai, zai fi dacewa mu kikiro wata jarrabawar, wadda za ta binciki cancantar dalibai wajen yin karatu a fannonin da suka zaba. Wasu tambayoyin kuma za su shafi masu son yin karatun digiri na 2 ne, saboda ga wannan nau'in na dalibai, ana bukatar su kai wani matsayi na ilimi a fanninsu kafin su iya karatu mai zurfin."

 • Kwanan wata 11.12.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnA
 • Kwanan wata 11.12.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnA