1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barzani ya bukaci majalisa ta warware rikicin PKK

November 5, 2011

Shugaban kurdawan Iraki ya nuna adawa da matakin soji da gwamnatin Turkiyya ta ɗauka akan 'yan adawan ƙungiyar PKK dake arewacin Iraƙi

https://p.dw.com/p/135kN
Ministan wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu da Massoud Barzani.Hoto: AP

Shugaban kurdawan Iraki Massud Barzani, ya nuna adawa da matakin soji da Turkiyya ta ɗauka domin yaƙar kurdawa 'yan adawa dake yankin arewacin Iraki, kasancewar hakan zai haifar da matsalar rashin samun mafitar din-din-din a wannan rikici. Tun a ranar alhamis ne Barzani ya isa birnin Ankara domin tattaunawa da magabatan Turkiyya dangane da  ci gaban yaƙar kurdawa 'yan fafutukar neman 'yanci na ƙungiyar PKK da sojojin gwamnati ke yi. Shugaban kurdawan Irakin yace, matakin soji ba shine mafitaba, a zauren majalisar Turkiyyan ya dace ayi mahawarar kawo karshen wannan takaddama. Tun a watan daya gabata ne dai, sojojin Turkiyya suka kutsa yankin arewacin Irakin da hare-hare akan kurdawa 'yan adawan, harin dake zama ramuwar gayya bayan kurdawan sun kai harin daya kashe sojojin kasar guda 24  a garin Cukurka dake kusa da kan iyakar Iraƙi. Kashe sojoji 24 ɗin dai ya kasance mafi munin asarar da gwamnatin Turkiyyan ta yi, tun daga shekara ta 1993. Tuni dai Priminista Recep Tayyip Erdorgan na Turkiyyan ya bukaci gwamnatin Barzani ta taka rawa wajen yaƙar kurdawan na ƙungiyar PKK.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita           : Usman Shehu Usman