1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barrow: Demokradiyya ta zauna a Afirka

January 21, 2017

Sabon shugaban Gambiya Adama Barrow ya yabawa yadda demokradiyya ta fara taka rawar gani a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/2WBFW
Gambia Machtwechsel - Präsident Adama Barrow in Dakar, Senegal
Hoto: Reuters/S. Shadid

Barrow na magana ne, a daidai lokacin da tsohon shugaba Yahya Jammeh ke shirin tattara yanasa yanasa ya fice daga kasar.

Barrow ya ce " abu ne mai muhimanci. Ina ganin demokradiyyar na samun gindin zama a Afirka, kuma hakan babban cigaba ne. Sauyi ne mai kyau wa Afirka. Kuma hakan zai yi tasiri a nahiyar".

Bayan tattaunawa na tsawon lokaci da shugabannin yankin yammacin Afirka, da barazanar yiwuwar amfani da karfin soji a kansa, da safiyar wannan Asabar din ce Yahya Jammeh ya sanar da cewar zai sauka daga mulki.

Sai dai har yanzu ba'a sanar da ranar da shugaba Barrowzai bar Dakar inda ya sha rantsuwar karbar mulki, zuwa Banjul babban birnin kasarsa ta Gambiya ba.