1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Barnar mahaukaciyar guguwar katarina

Alkaluma sun ce mahaukaciyar guguwar ta Katrina ta haddasa barnar da ta kai ta dala miliyan dubu 30

Mahaukaciyar guguwar katrina a Amurka

Mahaukaciyar guguwar katrina a Amurka

A dai halin da muke ciki yanzu an kiyasce cewar mahaukaciyar guguwar ta Katrina ta haddasa barnar da ta kai ta dalar Amurka miliyan dubu 30. An kwashe kusan dukkan mazauan garin New Orleans, wanda ruwa ya mamaye kashi 70% na harabarsa. Wannan mahaukaciyar guguwa ta Katrina ta bayyanar mana a fili ne cewar ruwa da iska na daya daga cikin abubuwan dake haddasa munanan bala’o’i a doron duniyar nan tamu. Wannan kuwa ba bakon lamari ba ne a can kudancin kasar Amurka. Guguwa mai dimi daga yankunan kurmi kann kwaso ruwa daga teku, inda lamarin kann tsananta daidai da zafin yanayi. Amma fa dan-Adam na da rabonsa na alhakin wannan bala’i daga Indallahi, sakamakon canje-canjen yanayin da yake haddasawa. Dan Adam ke fid da gubar nan ta Carbondioxid mai haddasa dimamar yanayi zuwa sararin samaniya. An kuma dadi kwararrun masana al’amuran yanayi na gargadi game da haka. Kuma ba karuwar yawan guguwar ne ake samu ba, illa kara tsananta da take yi. Amma duk da haka kwararrun masanan sun zama tamkar abin ba’a da dariya a idanun ‚yan siyasa, wadanda ke wa matsalar rikon sakainar kashi, duk da hakikancewar da suka yi da gaskiyar bayanan da masanan ke bayarwa. A farkon shekarun 1990 an yi zaton za a shiga wani sabon yayyi inda za a rika biyayya ga shawarwarin da kwararrun masanan suke bayarwa game da kayyade yawan gubar Carbondioxid da dan-Adam ke fitarwa zuwa samaniya, sakamakon taron bitar makomar yanayi na kasa da kasa da aka gudanar a Rio de Janeiro ta kasar Brazil. Amma nan da nan murna ta koma ciki saboda ba wani abin da aka tabuka na dakatar da wannan mummunan ci gaba. A maimakon haka sai hankali ya karkata ga wasu matsalolin dabam, wadanda suka shafi koma bayan tattalin arziki da ta’addancin da ya zama ruwan dare, a yayinda su kuma kasashe masu ci gaban masana’antu suka shiga kaka-nika-yi da matsalolinsu na tattalin arziki. A sakamakon haka aka sa kafa aka yi fatali da maganar kiyaye makomar kewayen dan-Adam kuma kasar Amurka ce ta farko da ta janye daga wannan manufa, musamman ma ganin cewar an gabatar da wasu tsayayyun matakan da suka cancanta a dauka. Ita kanta yarjejeniyar da aka cimma baya-bayan nan, bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi, babu wani haske tattare da ita. Domin kuwa an wayi gari ne ba wanda ke maganar kayyade sinadarin dake haddasa dimamar yanayin baki daya, saboda Amurka ta dage akan cewar faufau ba za a dama da ita a wannan manufa ba. A halin yanzu haka dai kasashen Turai da Amurka ne akan gaba wajen fitar da abubuwan dake haddasa dimamar yanayi, kuma nan ba dadadewa ba kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu irinsu Indiya da China zasu bi sau. Amma fa maganar kare makomar yanayi da kewayen dan-Adam ba magana ce ta alfarma ba, magana ce da ta shafi makomar rayuwar dan-Adam baki daya a doron kasa. Kuma mddin ba a nakalci lamarin da idanun basira aka kuma nuna halin sanin ya kamata ba, to kuwa barnar da zata biyo baya sai gyaran Allah kawai.