1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Barazanar yunwa tsakanin 'yan gudun hijira

Matsalar yunwa na kara tsananta a tsakanin jama'a, musamman wadanda ke samun mafaka a gidajen 'yan uwa da kuma wasu wuraren da ba sansanin 'yan gudun hijira ba.


Jama'a na fama da matsalar yunwa a a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, saboda matsalar karancin abinci da al'umma ke fuskanta musamman ma 'yan gudun hijira da ke zaune a gidaje ‘yan uwa da abokan arziki.

Kusan yawancin wadanda ke zaune a wuraren da sansanin 'yan gudun hijira ba ne, suna fuskantar wannan barazana ta yunwa inda ake iya ganin mutane a kyakushe wasu ma yunwar ta fara cin su.

Bayanai sun nuna cewar akwai ma wasu da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira da ke fama da wannan matsala. Bincike dai ya nuna cewa tsananin da jama'a ke fusknata da tattalin arzikin kasa da kuma raguwar tallafin abinci da ake samu shi ne ya haifar da wannan karancin abinci.

Tuni dai yanzu haka wasu kungiyoyin agaji suka fara gangamin neman taikamko don ceto mutane da ke fama da matsalar yunwa a jihar Borno.

Sauti da bidiyo akan labarin