1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar yunwa a yankin Sahel

September 10, 2010

Ana fuskantar barazanar yunwa a ƙasashe huɗu na yankin Sahel sakamakon ambaliyar ruwa

https://p.dw.com/p/P9N0
Yankin Sahel na fuskantar barazanaHoto: picture-alliance/ dpa

Da farko dai zamu fara ne da ya da zango a yankin Sahel, inda jaridar Neues Deutschland ta ce ƙasashe huɗu na wannan yankin na fuskantar barazanar faɗawa cikin wata mummunar masifa ta yunwa a daidai lokacin da hankali ya karkata zuwa ga ƙasar Pakistan. Jaridar ta ƙara da bayani tana mai cewar:

"Kimanin mutane miliyan goma a ƙasashe huɗu ke fuskantar barazanar yunwa, wadda ka iya zama irin shigen wadda aka fuskanta a shekara ta 2005 a ƙasar Nijer. Domin kuwa a baya ga ita kanta ƙasar ta Nijer, a wannan karon maƙobtanta da suka haɗa da Mali da Chadi da kuma Mauritaniya na fuskantar irin wannan barazana. Musabbabin haka kuwa shi ne ruwan da aka riƙa yi kamar da bakin ƙwarya, wanda ya ɓannatar da amfanin noman da yayi shaura daga farin da aka fuskanta a shekarar da ta wuce. Yara dai su ne suka fi shan raɗaɗin wannan matsala kamar yadda majiyoyi na asusun taimakon yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nunar."

A wannan makon Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito fili ta haƙiƙance kurakuran da sojojinta na kiyaye zaman lafiya suka caɓa a ƙasar Kongo. A lokacin da take rawaito wannan rahoton jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

NO FLASH Kongo
Sojojin MƊD a ƙasar KongoHoto: AP

"Babu wani abin da sojojin kiyaye zaman lafiya na Masjalisar Ɗinkin Duniya suka taɓuka don hana mummunar taɓargazar fyaɗe da aka riƙa yi wa mata a ƙasar Kongo. Wani abin lura ma shi ne kasancewar su kansu sojojin kiyaye zaman lafiyar na Majalisar Ɗinkin Duniya galibi akan same su da hannu dumu-dumu a ire-iren wannan taɓargaza ta fyaɗe a ƙasashen Afirka. Amirka dai ta ci alwashin kai maganar gaban kwamitin haƙƙin ɗan-Adam na majalisar, saboda wannan laifi ne da ya shafi illahirin ƙasashen dake da wakilci a Majalisar Ɗinkin Duniya."

An fuskanci zanga-zanga da tashe-tashen hankula a ƙasar Muzambik, sakamakon hauhawar farashin kaya a ƙasar dake zaman 'yar gaban goshin bankin duniya, in ji jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Mutane 13 suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen hankulan da aka yi tsawon yini biyu ana fuskanta a Maputo, fadar mulkin ƙasar Muzambik. Gwamnati ce dai ke ƙayyade farashin kaya kuma an ɗaga farashin burodi da ruwa da wuta da kuma mai sakamakon tashin darajar takardun kuɗin Rand na Afirka ta Kudu, wadda ita ce babbar abokiyar burmin cinikin Muzambik. An dai taɓa fuskantar rikici makamancin wannan a ƙasar a shekara ta 2008 lokacin da gwamnati tayi yunƙurin yin ƙarin farashi."

Mosambik Maputo Aufstände
Tashe-tashen hankula a Maputo ta MuzambikHoto: AP

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon bitar al'amuran tattalin arziƙin Afirka tayi tana mai bayyana mamakin yadda ƙasashen Turai dake maƙobtaka da nahiyar Afirka kai tsaye ke sako-sako da maganar zuba jari a wannan nahiya, wadda jaridar ta ce tana samun bunƙasar tattalin arziƙinta ba ƙaƙautawa.

Mawllafi:Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu